Ina manufar raba kan Hausawa da Fulani?

Daga MUS’AB MAFARA (phd)

To wai mai ɗan Arewa zai cimma a addinance ko a gwamnatance, ko a al’adance in an wayi gari yau an ce Bafillace daban, Bahaushe daban? Sannan, to ta ina ma za ka fara raba Hausawa da Fulani? Wai idan ka cire Fulanin rugga da wasu garuruwa a arewa-maso-gabas, wanne gida ne za ka tafi a Arewa da babu auratayya tsakanin Fulani da Hausawa?

Hausa harshe ne mai matuƙar tasiri ga waɗanda ke zaune cikinsa ta yadda kusan yawancin ƙabilun da ke yankin Arewacin Nijeriya sun zama Hausawa a magana da kuma a al’ada. Gaba ɗaya jikokin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da na sani a Sakkwato babu mai jin Fulatanci. Duka sun zama Hausawa.

Idan kuma na ɗauki misalin kai na, farkon zuwa na NYSC a Yola ‘Pullo monanta Fulfulde’ wato bafillacen da bai jin Fulatanci mutane ke ce min duk sadda su ka yi magana da Fulatanci ban mai da ba. A zahiri ina da ruwan Fulani ta gefen uwa amma ban taɓa jin ko ɗaya daga cikin kakanni na sun yi yaren ba balle mahaifiyata. To ta yaya zan ce wai bahillace ya zam abokin adawa ta don kawai wasu tsiraru daga cikinsu suna aikata laifi? Wannan kamar ka zargi duka Musulmi da ta’addanci ne don kawai Shekau da Abulƙaƙa da ma sauran ‘yan ta’adda suna kashe mutane da sunan Musulunci.

To amma mafi muni daga masu wannan kampe na ɓatanci su ne masu sukar jihadin Shehu Ɗanfodiyo da cewa wai faɗan ƙabilanci ne ba jihadi ba. Duk wanda ya karanci tarihin Shehu da muƙarrabansa to ba yadda za a yi ya zargi Shehu da ƙabilanci. Mutumin da ma sai da Duniyar ta zo bayan an yi galaba a kan ƙasashe da yawa amma ya zaɓi ya ba duniyar baya ya bar mulki hannun ƙaninsa da ɗansa, shi za a zarga da assasa ƙabilanci?

Sannan ai jama’a (sunan da a ke kiran mutanen Shehu da shi) sun ƙunshi Hausawa da Fulani da Azbinawa da sauran ƙabilun dake wannan yanki a wancan lokaci. Dukkansu sun goyi bayan Shehu saboda zaluncin sarakunan zamaninsu bai bar wata ƙabila ba. Sannan su suka zauna da Shehu kuma su ka gani a bayyane cewa wannan mutum don Allah yake yi ba don ƙabilarsa ba. Saboda me za su goyi bayan Shehu ya kawar da ƙabilarsu?

To amma wannan ba sabon abu ba ne, Manzon Allah (SAW) shi da ake yi wa wahayi ma an soke shi balle wani bawan Allah na daban. Allah Shi ke shiryar da mutane a kan abunda yake dai-dai, amma riƙonmu da addini a arewanci Najeriya tabbas akwai tasirin jihadin Shehu Ɗanfodiyo da magoya-bayansa sosai a ciki. Kada ka saurari duk wanda zai sa ka kalli kowanne bafillace a matsayin maƙiyinka. Tabbas ka ƙi Turji da ire-irensa, amma duk bafillacen da bai nufe ka da sharri ba ka cigaba da alaƙarka da shi kamar yadda muke yi kaka da kakanni.

Wannan kamfe ne kawai na ‘yan soshiyal midiya tare da majivintansu su Nnamdi Kanu, waɗanda fatarsu su ga mun samu ɓaraka a tsakaninmu. Wato tun da an raba ‘yan ‘middle-belt’ da Hausa-Fulani to bari a raba tsakanin Hausa da Fulanin su ma. Kada ka biye mu su.

Musab Mafara ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi.
Imel: [email protected]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *