Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Allah ya gaya mana cikin Qurani cewa a ranar da za’a tashi kiyama, wani Kaho za’a busa wanda zai halaka dukkan halittu masu Rai da mara Rai (face yan kalilan) a cikin sammai da ƙassai; Q39:68 “Kuma aka busa a cikin ƙaho, sai waɗanda ke a cikin sammai da ƙasã suka sũma sai wanda Allah Ya so (rashin sumansa) sa’an nan aka hũra a cikinsa, wata hũrãwa, sai gã su tsaitsaye, sunã kallo.”
Wato tashin alkiyama, ko muce karshen duniya/sammai (universe) wadda ta faro kimanin shekaru biliyan 13.8 (ko biliyan 28 sakamakon wasu sabbin alkaluma na James Webb Telescope), zai zo nan gaba (Wanda shi ma a ke hasashen nan da wasu shekarun biliyan 20 ko fiye). Allah ya shaida mana a aya ta sama cewa wata Kara ce mai tsananin karfi wadda tana aukuwa, dukkan halitta a kaunu (physical) da kuma masu rai ciki (face kalilan) da Allah ya kebe kadai ne ba zasu mutu ba a wannan lokaci.
To, kamar yadda Allah ya fada, binciken kimiyya ya gano cewa shi karar sauti (sound) wanda ake auna shi da ma’aunin Decibel wanda aka fara sikelinsa daga sifili (zero), wanda ya yi daidai da shiru a wani waje babu ko motsin iska, wannan shine awon Decibel dB 0. Karuwar wannan yanayi sakamakon sauti shine ke daga ma’aunin daga sifili ya yi ta yin sama ya na karuwa. Misali sautin magana ba ya wuce dB 60, na karar ababen hawa a bakin titi, ko injin yanke ciyawa ko na markade baya wuce dB 85, wanda dadewa ana sauraron irin wannan kara zai iya lahani ga jin mutum. Ko Kuma na tashin jirgin sama, ko karar harba bindiga mai dB 140.
To, yanzu masana kimiyya, kamar yadda wannan bidiyo yayi bayani, karar dB 1100 za ta hallaka dukkan sammai da kassai a lokaci guda ta hanyar haifar da Black hole, wato bakar tauraruwa da za ta zuke dukkan sammai a lokaci guda ta dunkule waje guda. Kamar yadda Allah ya ce mana cikin Suratul Yasin; Q36:29 “Ba ta kasance ba face tsawa guda, sa’an nan sai gã su sumammu.”
Wato da zarar Allah ya daga ma’aunin Decibel zuwa 1100, nan take kowa zai halaka kamar yadda wannan bincike ke bayani. Kuma duk kaunu ta kasance; Q21:104 “A rãnar da Muke naɗe sãma kamar neɗẽwar takarda ga abũbuwan rubũtãwa kamar yadda Muka fãra a farKon halitta Muke mãyar da ita. Wa’adi ne a Kanmu. Lalle ne Mun kasance Mãsu aikatãwa.”
Wato sammai gaba daya wadda a yanzu ke fadada da tsananin gudu na 74persec, za ta ja burki kenan ta dawo baya ta dunkule, abinda masana kimiyya ke kira da “Big Crunch” wato komai za’a matse shi ya dunkule waje guda. Kamar yadda a farko lokaci daga irin wannan dunkule wanda ya tarwatse (Big Bang) shine ya haifar da samuwar wannan sammai. To karshenta kuma shine wannan nadewa (Big Crunch).
Shekaru 1400 a Qurani Allah ya bayyana mana yadda wannan kaunu ta mu zata zo karshe, amma sai a Yan shekarun nan kuma kimiyya ta ke bayyana mana a zahirance yadda abin zai wakana ta hanyar bincike. Tsarki ya tabbata ga ubangijin halitta.
