Da Ɗumi-ɗumi: Shugaban Jamiyyar PDP na Zamfara ya rasu

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau,

Allah Ya yi Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Zamfara, Hon. Ahmad Sani Kaura rasuwa.

Majiya ta kusa da iyalan marigayin ta tabbatar wa wakilinmu da rasuwar ta wayar tarho.

Majiyar ta ce, marigayin ya mutu ne a ɗaya daga cikin cibiyoyin kiwon lafiya a jihar bayan doguwar jinya.

Ƙarin bayani na nan tafe…