Saƙon da muke so mambobinmu na ƙungiyar TIGMEIN su fahimta

Manhaja logo

Daga MAHADI SHEIKH SUFWAN

Babban jagoran ƙungiyar qara samun haɗin kan tijjanawa da tallafawa juna TIGMEIN na ƙasa, Sheikh Tijjani Sheikh Sani Auwal Inyas. Da shugaban kwamitin amitattu na ƙasa Dakta Ibrahim Umar Pandogari, da sauran majalisar shugabanni na ƙasa, Suna miƙa saƙo na musamman ga dukkan shugabannin TIGMEIN na jihohi da ƙananan hukumomi da mazaɓu kamar haka, ganin cewa gwamnatin Nijeriya ta bayar da izini ga jam’iyyun siyasa su fara gudanar da yaƙin neman zaɓe a ƙasa bakiɗaya, wannan kungiya tana umurtar dukkan shugabanni su kula da abubuwa kamar haka:

  1. Wayar da kan dukkan tijjanawa wajen kauce wa dukkan wani nau’i na amfani da su wajen bangar siyasa da ta’addanci wanda tuntuni da ma ba a san mu da shi ba
  2. Kada mu sanya aqidar son wata jam’iyya a gaba, face mun samu dukkan mutumin da aka tabbatar ya cancanta, kuma mu tijjanawa muna da cikakkiyar qima a wajensa.
  3. Wajibinmu ne mu zauna da ɗan takarar kowacce kujera idan ya buƙaci haka domin a faɗa masa buƙatunmu na tijjanawa kuma mu ji manufofinsa a kan gudanar da mulkin kujerar da yake nema,
  4. Idan an gamsu da ɗan takara bisa yarda da buƙatunmu tare da amincewa da manufofinsa, to a yi gaggawar sanar da shehunnamu da jagororin zawiyyoyinmu, na yankunanku.

Muna godiya bisa yadda shuwagannin wannan ƙungiya na dukkan jihohin Nijeriya da ƙananan hukumomi suke gudanar da ayyukan wannan ƙungiya bisa tsari da bin manufofinta musamman wajen ƙoƙarin tallafa wa junanmu da jajircewa wajen kare mutuncin tijjanawa a kowacce fuska.

Daga ƙarshe, muna ƙara jaddada nasiha ga matasanmu wajen tsayawa a kan turbar da aka san mu ta zaman lafiya da kauce wa dukkan wani nau’i na saɓa wa doka.

Sannan muna kira ga shugabanni da su ƙara kusantar shehunnanmu da zawiyyoyinmu wajen cigaba da addu’oi, Allah ya sa a yi zaɓuɓɓuka lafiya, ya ba mu shugabanni nagari masu adalci, kuma masu son cigaban ƙasarmu. Muna godiya.