Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya ce yana mai ƙwarin gwiwa kuma da yardar Allah shugaban ƙasa Bola Tinubu zai sake lashe zaɓe a 2027.
Dikko Raɗɗa ya faɗi haka ne a mazaɓar sa na garin Raɗɗa da ke ƙaramar hukumar Charanchi inda ya kaɗa ƙuri’ar sa a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa.
Ya bayyana cewa alummar jihar Katsina uwa ɗaya uba ɗaya ne duba da yadda zaɓuɓɓukan na cikin gida a jam’iyar APC ya gudana, domin haka gwamnan ya ce yana mai tabbacin cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ne zai sake lashe zaɓe.
Tsohon gwamnan jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema a wata hira da manema labarai a gidan sa da ke Dutsinma ya nuna gamsuwar sa ga yadda zaɓen fidda gwani na jam’iyar ya gudana a mazaɓar sa ta Shema.
Ya ce yadda yaga dandazon ya’yan jam’iyar APC a mazaɓar na nuna masa da yardar Allah, yadda aka fito zaɓar APC a zaɓen 2023 hakama tarihi zai maimaita kansa.
Akan zaman sasanci ƙarƙashin kwamitin da yayi mata mataimaki, Shema ya bayyana cewa kwamitin ya zauna da yan takarar da basu sami nasara ba kuna an tattauna tare da basu hakuri bayan da kwamitin ya saurari ƙorafe ƙorafen su.
Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa kwamitin ya saurari ƙorafe ƙorafe tare da turawa Gwamnati da shawarwarin kwamitin domin ɗaukar mataki.
Ya shawarci yan takarar da suka sami nasara da su ziyarci yan uwansu da ba su yi nasara ba domin sasantawa da ban hakuri da kuma bi gida gida domin tallata jam’iyar kan zaɓe mai zuwa.
