Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙungiyar cigaban Funtua ta shirya karrama Sarkin Maska Idris Sambo Idris Hakimin Funtua da lambar Yabo.
Shugaban ƙungiyar kwamred Mannir Suleiman ya faɗi haka a wata hira da manema labarai a Katsina.
Ya bayyana Sarkin Maska a ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki da su ka kawo gagarumin cigaba a yankin musamman a garin Funtua inda yake hakimci.
Kwamred Suleiman ya ce a tsowan shekaru 30 yana Hakimin Funtua,garin ya samu cigaban da ta zama babban birni da za ta yi gogaiya da manyan birane a jihohin ƙasar.
“A lokacin Sarkin Maska, ya bada gagarumin gudummuwa wajan ganin garin Funtua ta sami jami’a,manyan tagwayen hanyoyi,ɗaukaka darajar ƙananan asibitoci zuwa manya da bunƙasa wajen harkar kasuwanci,”Inji kwamred Suleiman.
Haka kuma Sarkin Maska ya ƙarfafa zumunci a tsakankanin alumma da bunƙasa kasuwanci a yankin a cewar shugaban ƙungiyar.
“Sarkin Maska shine Hakimin da a koda yaushe ya kan Kai ziyarar kyautata zumunci da tabbatar da dauwamamman zaman lafiya ga alummar sa,”Inji kwamred Suleiman.
Akan haka ne Inji shugaban ƙungiyar da sauran wasu abubuwan alheri da yake aiwatar wa a fadar sa,ya sa ƙungiyar ta ga ya dace ta karrama Hakimin da lambar yabo don ƙara masa ƙarfin gwiwa da ya cigaba da gudanar da irin waɗannan hidima ta alheri yankin.
Ya ce nan gaba bada jimawa ba za a sanar da ranar karramawa.
