Matawalle ya yi gangami a Zamfara domin tabbatar da Tinubu a matsayin ɗan takarar APC

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma ministan tsaro, Mohammed Bello Matawalle, a yau Asabar ya jagoranci dubban magoya bayan Jam’iyyar APC a wani gangamin nuna goyon bayan su ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu a 2027.

Taron, wanda aka gudanar a Maradun mahaifar Matawalle, ya jawo ɗimbin jama’a masu goyon bayan jam’iyyar waɗanda suka sake jaddada jajircewar su ga APC da gwamnatin Tinubu kafin babban zaɓe mai zuwa.

A jawabinsa ga taron jama’a, Matawalle ya ce yawan waɗanda suka fito ya nuna ƙaruwar amincewa da jama’a ga gwamnatin tarayya da jam’iyyar APC ke jagoranta da kuma ƙarfin dimokuraɗiyya a faɗin jihar.

Ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa Shugaba Tinubu da ‘yan takarar APC a duk faɗin ƙasar za su samu nasara mai kyau a 2027.

“Yawan waɗanda suka fito a nan a yau alama ce bayyananniya cewa mutanen Zamfara suna goyon bayan APC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu,” in ji Matawalle.

“Muna da ƙwarin gwiwar cewa jam’iyyar APC za ta samu gagarumar nasara a dukkan muƙamai na zaɓe a jihar.”

Taron ya kasance wani ɓangare na ayyukan wayar da kan jama’a da jam’iyyar ke gudanarwa, inda ‘yan jam’iyyar suka amince da sake tsayawa takarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a bainar jama’a.

Matawalle, ya sake nanata cewa Zamfara za ta ci gaba da kasancewa cibiyar APC kuma za ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da ƙuri’u ga jam’iyyar a zagayen zaɓe mai zuwa.

By ukarofi