
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Manchester City ta tabbatar da cewa kocin ‘yan wasanta, wato Pep Guardiola zai bar kulob ɗin a ƙarshen kakar wasan bana.
Ɗan Sifaniyar mai shekaru 55 ya sanar da haka a ranar Juma’a ta wani faifan bidiyo, inda aka gan shi cikin halin takaici yana wa magoya bayan ƙungiyar jawabi, lamarin da yak kawo ƙarshen zamansa a kulob ɗin na tsawon kusan shekara goma.
A cewar BBC Sport, Man City ta fara shirye-shiryen ɗauko wani koci tun tsawon shekara guda gabanin ƙarewar kwantaragin Guardiola.
A gobe Lahadi ne Guardiola zai jagoranci wasansa na ƙarshe a ƙungiyar kuma na ƙarshe a gasar Premier League da za a yi tsakanin City da Aston Villa.
A jawabinsa, ƙwararren kocin ya yi godiya ga ƙungiyar da magoya bayanta bisa dama da gudunmawar da suka ba shi har ta kai ga ya cimma nasarori da dama.
A ƙarƙashin jagorancinsa, Manchester City ta lashe manyan kofuna da suka haɗa da Premier League guda shida, Champions League ɗaya da dai sauransu, inda ya lashe jimillar kofuna 20.
Ga jerinsu kamar yadda IntelRegion ta ruwaito:
League Cup (2018)
🏆 Premier League (2018)
🏆 Community Shield (2018)
🏆 League Cup (2019)
🏆 Premier League (2019)
🏆 FA Cup (2019)
🏆 Community Shield (2019)
🏆 League Cup (2020)
🏆 League Cup (2021)
🏆 Premier League (2021)
🏆 Premier League (2022)
🏆 Premier League (2023)
🏆 FA Cup (2023)
🏆 Champions League (2023)
🏆 Super Cup (2023)
🏆 Club World Cup (2023)
🏆 Premier League (2024)
🏆 Community Shield (2024)
🏆 League Cup (2026)
🏆 FA Cup (2026).
