Dabarun ƙasar Sin na kiyaye yankuna masu dausayi ga zuriyoyi da ke tafe

Daga CMG HAUSA

A jiya Asabar ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, yayin bikin buɗe taron wakilan ɓangarorin da suka sanya hannu kan Yarjejeniyar Ramsar, kan yankuna masu dausayi ko COP14 a takaice, wanda aka yi a birnin Wuhan, inda ya jaddada cewa, ya dace a kara samun fahimta, da fadada haɗin-gwiwa, domin ɗaukar matakan kiyaye yankuna masu dausayi a faɗin duniya baki daya.

Shugaba Xi ya bayyana wasu ra’ayoyi uku, dangane da aikin kiyaye yankuna masu dausayi, al’amarin da ya tsara shirye-shirye ga kiyaye yankuna masu dausayi a duk duniya.

A wajen babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20 da aka yi kwanan baya, an bayyana manufar farfado da al’ummomin ƙasar Sin daga dukkan fannoni, bisa zamanintar da ƙasar mai sigar musamman, kuma “kasancewar dan Adam, da muhallin halittu cikin jituwa” daya ne daga cikin wasu muhimman halaye biyar na zamanintar da ƙasar mai sigar musamman.

A cikin jawabin, shugaba Xi ya kuma gabatar da muhimman matakan da ƙasarsa za ta dauka a nan gaba, a fannin kiyaye yankuna masu dausayi, waɗanda ke shaida cewa, ƙasar Sin za ta ci gaba da himmatuwa wajen shimfida zaman jituwa tsakanin dan Adam da muhallin halittu, da raya sha’anin kare yankuna masu dausayi ta hanyar da ta dace.

Mai fassara: Murtala Zhang