Daga ƙarshe, ɗan takarar APC Oyebamiji ya magantu bayan kaye a zaɓen Osun

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan takarar gwamnan jihar Osun a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, ya magantu a karon fari bayan shan kaye a hannun gwamna mai ci, Ademola Adeleke a zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar.

Oyebamiji ya karɓi sakamakon da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fitar yayin da ya koka kan zargin hare-haren da aka kai wa wasu mambobin APC da magoya baya bayan zaɓen.

An sanar da Adeleke na jam’iyyar Accord Party a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan samun ƙuri’a 511,067, yayin da Oyebamiji ya samu ƙuri’a 444,815 a matsayi na biyu.

A wani rubutu da aka wallafa ta sahihin shafinsa na X a ranar Talata, Oyebamiji ya yi godiya ga jagororin APC, mambobi, magoya baya, ‘yan sa-kai da masu zaɓe bisa ƙoƙarinsu a baki ɗaya lokacin yawon neman zaɓensa.

Tsohon kwamishinan ya ce jam’iyyar ta yi fatan wani sakamako da ba wannan ba, amma za ta girmama matsayar hukumar zaɓe yayin da take nazarin sakamakon.

Ya bayyana cewa, yawon neman zaɓe da zaɓen ba za su kawo ƙarshen ababe da ƙa’idojin da suka ba wa lamuran siyasarsa kariya ba, yana mai alƙawarin cigaba da kira ga samar da ababen ci-gaban masu ɗorewa a sassan jihar.

Oyebamiji ya kuma koka akan zargin kai wa wasu ‘yan APC farmaki, inda ya ce hakan ya yi ƙamari musamman ana saura kwana guda a yi zaɓe.

Akan haka ne ya yi kira ga Rundunar ‘Yan Sanda da sauran hukumomin tsaro da su shiga tsakani don bai wa mazauna kariya musamman mambobin APC da magoya baya da ake zargin ana kai wa farmaki.

By Babaji

Leave a Reply