
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar ƴan kasuwar man fetur (IPMAN) ta ce farashin kowacce lita za ta koma N935 daga ranar Litinin la’akari da sabon tsarin da Kamfanin Ɗangote ya yi.
IPMAN ta ce tunda kamfanin Ɗangote ya rage farashi hakan ya sa take ganin dacewar a samu tsari na bai-ɗaya daga gidajen man ƴan kasuwar a faɗin Nijeriya.
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Maigandi Garima ya bayyana hakan a ranar Lahadi, yayin hira da kamfanin dillancin labarai (NAN) inda ya jinjina wa ci-gaban da aka samu daga Ɗangote.
A ƴan kwanakin nan ne Kamfanin Ɗangote ya sanar da rage farashin da kaso 7.27 inda ya koma N899.5 daga N970 kuma ya haɗe kai da Kamfanin MRS don cimma matsaya game da farashin.
Hakan na zuwa ne a lokacin da al’umma ke shirin gudanar da bukukuwan ƙarshen shekara.
