Daga BELLO A. BABAJI
Sufeto Janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun ya yi gargaɗi game da hargitsi da rashin tsaro da ake samu wajen raba kayayyakin tallafi ga mutane a yayin bikin Kirismas.
Sufeton ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Kakakinsa, Muyiwa Adejobi ya fitar, inda ya ce duk wanda aka samu da sakaci a ɓangarensa yayin irin aikin, za a kama shi da aikata babban laifi.
Egbetokun ya koka kan rashin tsari dake tattare da irin aikin wanda ya haddasa asarar rayuka da dama a Nijeriya musamman a irin wannan lokaci na bukukuwan ƙarshen shekara.
A ranar 18 ga watan Disamba ne wani lamarin alhini ya auku a Ibadan, babban birnin jihar Oyo inda aka rasa rayuka 35 a wajen shaƙatawa waɗanda galibin su yara ne ƙanana.
Haka ma a ranar Asabar a Abuja an rasa rayuka guda 10 da jikkata da wasu suka yi a yayin rabon kayayyakin tallafi a wani cocin katolika dake unguwar Maitama.
Kamar haka ya kuma faruwa a yankin Okija na jihar Anambara wajen rabon kayan tallafi inda mutane 12 suka rasa rayukansu.
Don haka ne Sufeton ya gargaɗi ƙungiyoyi da masu shirya ire-iren ayyukan da su tabbatar da sun yi tsari da zai kula da lafiyar al’umma gabannin su fara aiwatarwa, ya na mai cewa za a hukunta waɗanda suka bijere wa kalaman nasa.
