Kasafin 2025: Gyaran makwancin Tinubu da Shettima zai lashe Naira biliyan 6.36

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Tarayya ta ware zunzurutun kuɗaɗe da adadinsu ya kai N6,364,181,224 don gyaran gidajen zaman Shugaba Bola Tinubu da na Mataimakinsa, Kashim Shettima da kuma na wasu manyan muƙarrabansu a kasafin kuɗin shekarar 2025.

Haka kuma rahotanni sun bayyana cewa kuɗin gyaran Fadar shugaban ƙasa dake Abuja, za ta riƙa lashe Naira biliyan 5.49 kamar yadda yake a ƙudirin gyare-gyare na 2025 da aka gabatar wa majalisa.

Daga cikin kasafin, za a yi amfani da miliyan N765 wajen gyaran gidan da mataimakin shugaban ƙasar yake zama da kuma masauƙinsa.

Gyaran sashin da Shugaba Tinubu yake zama a Fadar shugaban ƙasa kuwa zai lashe miliyan N6.39 yayin da kuma ɓangarorin jami’an tsaro, ɗakunan taruka da sashen mataimaka za su lashe miliyan N49.

Bugu da ƙari, Barikin Prescott na jami’an Maple State House da ofishin Sigina dake Asokoro a Abuja, za su lanƙwame miliyan N51.

Sannan, kasafin ya ware Naira miliyan 87 ga Shugaba Tinubu da Mataimakin nasa a matsayin karramawa da kuma alawus na zama yayin da miliyan N127 za a yi amfani da su ne wajen sayen SUVs.

Har’ilayau, za a sayi ababen hawa akan kuɗi Naira biliyan 3.66.

Sai kuma biliyan 14.72 na gyaran Fadar shugaban ƙasa dake Legas da masauƙin Mataimakin shugaban ƙasa na Ikoyi da suaran su.

By ukarofi