
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Ci-gaban Ma’adinai, Dele Alake ya faɗi hakan yayin hira da manema labarai a ranar Lahadi, kamar yadda Kakakin Ma’aikatar, Segun Tomori ya bayyana.
Ministan ya ce gwamnati ta yanke soke takunkumin haƙar ma’adanan ne la’akari da yadda ake samun ci-gaba game da halin tsaro a jihar.
Alake ya bayyana cewa akwai riba sosai ga Nijeriya a irin ma’adanan da Zamfara take da su waɗanda suka haɗa da Gwala-gwalai, ‘Lithium’ da ‘Copper belts’.
Ya kuma ce an dakatar da ayyukan haƙar ne sakamakon samun waɗanda suke bi ta haramtattun hanyoyi acikin masu haƙar wanda hakan ke haifar da koma baya ga harkokin gudanarwar gwamnati.
Zamfara tana da kaso mai girma acikin jihohin da ke samarwa Nijeriya kuɗin shiga mai yawa, kamar yadda Ministan ya bayyana.
A shekarar 2019 ne Gwamnatin Tarayya ta umarci a dakatar da ayyukan haƙar ma’adanai a jihar sakamakon barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma saboda rashin tsaro da Zamfara da yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya ke fuskanta.
