Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Wato idan ka tsaya tsai, ka kalli yadda biki na aure (ko ma na mutuwa, tunda shi ma ya zama biki) hakika za ka gane irin tunanin mutanenmu na Arewa, musamman shugabanninmu. A tarihin Kano ba na jin an taba biki da facaka da nuna izza da almubazzaranci irin bukukuwa biyu da muka gani cikin Yan shekarun nan. Kuma abubuwa uku dole ga duk mai nazarin halin da ake ciki ya koka da su.
Na farko shine yadda manyan Arewa su ke bautawa bikin yayansu fiye da duk wani abu na zamantakewar al’ummar da su ke mulka. Domin da zarar wane fitacce zai aurar, to duk inda wani fitaccen Dan Arewa ya ke, ko a kasar wajen yake zai gaggauta tahowa ya halarta, wato zai iya soke komai domin tabbatar da cewa ya shaida an ganshi a taron. Haka zalika, a yayin taron bikin duk wani banbanci na bigi-bagiro a siyansance, kabilance ko a addinance ba ka ganinsa a wajen. Zaka sami wadannan manya namu sun zama uwa-daya, uba-daya babu bambanci.
Bukukuwa biyu da nake magana sun kafa tarihi a Kano sune wanda aka yi na auren Dan Shugaba Buhari ya na mulki da Yar gidan sarautar Kano. Wannan biki sai da ya kafa wa filin jirgin saman Malam Aminu Kano tarihi na kasancewa ya tara jiragen sama kusan tamanin a lokaci guda, abinda a tsawon shekaru sama da hamsin na filin bai taba gani ba. Sannan a kwanan nan mun ga bikin auren Yar Kwankwaso wanda ake maganar siyen baki da mahaukatan kudade. Wannan facaka ba wani abu bace da ace a wadatacciyar al’umma ce, amma wannan na faruwa ne a lokacin da mutane su ke kasa iya cin abinci sau uku.
Mafi takaici shine, wannan facaka fa an yi ta ne karkashin mutane biyu wadanda a fadin Arewa kaf babu wasu mutane da Allah ya yi wa ni’imar magoya baya wadanda ke musu kauna da biyayya kamar ta bauta, ba tare da wadannan shugabanni na iya basu ko sisi ba. Shin wadannan shugabanni ba su ci amanar kauna da biyayyar talakawan nan ba? Shin soyayyar tasu ga talaka ta Allah da Annabi ce?
Idan irinsu Dangote ne su ka yi wannan facaka, ka ce ai su Yan kasuwa ne, kudinsu a kasuwanci su ka samu. Amma mutanen da a kullum su ke nuna cewa talakawa su ke wa yakin samar musu da rayuwa mai kyau, wanda hakan ya gagara, sannan su rika tsokanewa talaka ido ya hanyar wannan facaka? Hakan ya yi kama da tausayi ko ma jin kunyar talakan?
To, alhamdulillah dai, an ce da na gaba a ke gane zurfin ruwa. Ko wanene kai ba za ka taba samun makauniyar biyayya da kima irin wadda Buhari ya samu a kasar nan ba, amma da yake Allah ya san cewa ba talaka ne a zuciyarsa ba, mulkin kawai ya ke nema, tunda shi Allah ba a yaudararsa, don haka sai ya baiwa Buhari mulki da koshin lafiya na tsawon shekaru takwas domin yayi masa tsirara har sai da kowa ya ganshi a zahirinsa. Shi ma Kwankwaso ya biyo wannan hanya ta Buhari, domin duk da abin takaici da aka yi masa da mutanen Kano a 2019, sai Allah ya tsayar da shi da kafarsa, shi kadai ya kada masu jin su na da karfin gwamnati. Amma maimakon ya tsaya ya tabbatar da cewa ya biyawa mutanen Kano bashin mika masa amana, sai aka bige da rusau ta ramuwa daga shigowa gwamnati. Allah ya sake nusar da shi kan ya tsaya bisa adalci ta hanyar barazanar sake kwace zabe a kotu, wanda shi ma Allah ya tserar da shi da gwamnatin. Maimakon shukura a dora da aiki sai aka dawo da rigimar masarauta. Wasa-wasa shekaru biyu sun balbalce ba wani abin a zo a gani a gwamnati, kuma daga badi an shiga maganar zaben 2027. A wannan tsanani da Tinubu ya haifar a kasar kuma ya jagoranci irin wannan biki na Allah-tsine-uwar-mai-karya.
A ƙarshe, Ina kyautata zaton cewa a yau Buhari na Daura ya na da-na-sanin abubuwa da dama, to amma Kwankwaso har yanzu ya na da wata dama na gyarawa idan ya so. Lokaci ba ya jiran kowa, kuma babu wanda zai iya yaudarar Allah sai dai ya yaudari mutane ko kansa, kuma dai karshen kowace irin yaudara…nadama ce.
Haba ‘yan siyasa me Barau Jibrin ya yi ne?
Ina ga kamata yayi muyi tsokaci game da balahirar dake faruwa cikin da’irar siyasar jihar Kano. Nake ga kamata yayi ‘yan siyasar jihar Kano suyi la’akari da yau da gobe domin gane gaskiyar burin jama’ar jihar Kano. a yau siyasar jihar Kano ta shiga wani yanayi marar daɗi, saboda balagazar dake faruwa ta rashin girmama juna. Babban abu shine a yau siyasa ta zama harkar ramuwa koda kuwa hakan zai shafi wanda bai ji ba, bai gani ba. A Kano ne akayi rushe-rushe domin wai waccan gwamnati haramtacciya ce, ikon Allah, ban san ranar da gwamnatin da aka zaɓa ta zama haramtacciya ba? Duk faɗin Nijeriya babu inda siyasa tayi tsami kamar jihar Kano, domin kuwa banga inda ake bita da ƙulli ba kamar jihar Kano, saboda irin rashin fahimtar dake faruwa tun lokacin da sabuwar gwamnatin Kano ta yanzu take yi ba. Ni dai nasan cewa, mun sami gwamnatoci biyu kuma na PRP sun shiga irin wannan fitinar siyasa wato ta ƙiyayya, wacce take a bayyane!
Yanzu duk wani abu za’a iya gani, siyasar Kano ta musgunta domin rushe-rushe da akayi da kuma zage-zage da ake gani ra’ayal aini, yau babu wani mutum da ba’a zaga ba komai girmansa, cikin wannan mummunan hali da jihar Malam Aminu Kano ta sami kanta a ciki! Yau duk mutumin kirki ya kama bakinsa yayi shiru, saboda yau ‘yan siyasa sun koma masu yaɗa alfasha kamar ‘ya’yan ‘yan gambara waɗanda ko iyayensu basa jin kunyar yiwa ba‘a! Wal iyazubillahi, kaji dai yadda siyasar Kano ta juye cin mutuncin masu matunci. Ababe biyu ne suka jirkita siyasar Kano, kawai saboda akwai wanda yake gani shi kaɗai ne ya gaji jihar gaba ɗayanta, saboda haka duk wanda zai shigo cikin da’irar siyasa sai ya shigo ta ƙafarsa, in kuwa ba haka ba, to zai gamu da ƙalubalen siyasa na zage-zage da cin fuska babu gaira babu dalili.
Ban san inda Kano ta gaji wannan halayya ba, akwai gwamnan da ya fito tsatson wancan gefen a 2015, kuma yaƙi yarda a juya shi yadda ake so, wannan shine sanadin gaba har yau ɗin nan kuma sharri da wulaƙanci, shi ya bishi har kuwan yanzun nan, wannan dame yayi kama siyasar ko yahudanci? Naji naga anata surutai akan Malam Barau Jibrin sukan da ba zaiyi wani tasiri ba, nasan dai siyasa irinta Nijeriya akwai zulaya da zulaƙe, saboda haka abu ne a bayyane cewa ‘yan siyasa kususan a nan arewa suna laɓewa a doron ƙarya domin toshewa gaskiya ta sami ɓugar da zama a cikin lumana. Sanata Barau a dukkan arewa ta yau ya zama guga mai bada ruwan zam-zam, domin kowa yasha ya sami sauƙin cututtukan da can dana yanzu.
Na ke ganin ‘yan siyasa masu wayo basa buƙatar ace yau wato yau an sami mai son kyautatawa rayuwar al’umma ba, sai dai su laɓe a bayan jama’a su ɓoye komai daga su sai ‘ya’yansu ko kuma suje Dubai su buɗewa ‘ya’yansu kantuna, a nan kuma su saka ‘ya’yan talakawa cikin kuskunda da shan kayan maye, domin kada suma su zama masu amfanar da kansu. Barau Jibrin tun yana ɗan majalisa wato ɗan majalisar wakilai ta tarayyar Nijeriya, yake kawo abubuwan cigaba a mazaɓarsa ta Tarauni. Ya yi fice ainun wajen kawo abubuwan more rayuwa waɗanda zasu taimakawa al’umma tun wancan lokaci, balle yanzu da yake ɗan majalisar dattijai. Kaga dai bashi da tsara a Chambar Dattijai sai dai akwai dattijo kuma matashi wanda ya fito daga mazaɓar Sumaila shima Goga ne wurin taimakawa jama’a, gaskiya shi Barau ya nuna shima kowa ne, domin ayyukansa sun nuna haka, domin ba inda bai taɓo ba, tun daga ƙananan hukumominsa sha uku (13) harma ko’ina a jihar Kano, saboda wannan himma tasa sai kawai yayi kiciɓis da maƙiya hagu da dama, domin kawai shi ba mugu bane, bashi da halin daga shi sai ‘ya’yansa. Kowa ya san duk masu yaɗa furofaganda masu buƙatar arewa ta zauna har abada a baya, domin idan ɗansu ya samu mulki anta yi masa bita da ƙulli kenan, har sai ya kasa ababen alheri da yake so ya yiwa Nijeriya!
Mun ga haka akan marigayi General Sani Abacha da kuma mutumin kirki wato Shiekh Umaru Musa Yar’dua wanda ya yi ƙoƙarin yaga talakawa sunji daɗi, kususan wurin sayen Man Fetur, menene ya faru domin hakan ta faru? Marigayi Yar‘dua da Janar Abacha da marigayi Shehu Aliyu Shagari dukkansu niyyarsu shine kyautatawa Nijeriya da ‘yan Nijeriya, wacce irin turjiya ce basu gani ba, ga waɗanda yanzu suke balagaza gashi Dakta Barau Jibrin; Duk wani mai maganar arewa baifi Alhaji Shehu Aliyu Shagari da Alhaji Umaru Musa Yar’dua da Janar Abacha ba. Allah Ya jiƙan bayinsa, mutanen da suke buƙatar kawo cigaba ga Nijeriya, amma yaya suka ƙare da halayen mutanen da yanzu suke ƙalubalantar Maigirma shugaban talakawa a Nijeriya wato Barau Jibrin.
Abin baƙin ciki ma shine, yadda wasu malamai kawai suka cika duniya da ayyururi na zagi da muguwar addu’a ga wannan bawan Allah kawai domin ɓata masa suna, kai Allah Ya kiyaye mu da ‘yan mashalo; Ashe suna nan ake tayiwa talakawan Katsina, Zamfara, Sokoto, Neja da Kaduna kisan mummuƙe, sai kawai zancen harajin da ya shafi ɓoyayyun kamfanoninsu shine zasu fito domin ƙalubalantar Barau haka kawai. Allah Ya sa abinda suke nufi ba haka yake ba mu ga inda za su sa kansu.
Naku Comrade Ibrahim Abdu Zango
Shugaban Kano Unity Forum, No. 260, Zango ƙuarters, Kano, Jihar Kano, Nijeriya, 081754722983rd December, 2024
