Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya tabbatar da cewa dakarun sojin Nijeriya sun samu gagarumar nasara wajen fatattakar daruruwan ’yan bindiga tare da ruguza sansanoninsu a wasu samame na hadin gwiwa da aka gudanar a fadin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala wani taron tsaro na sirri a fadar gwamnatin jihar da ke Bauchi. Ya ce an samu wannan nasara ne sakamakon hadin gwiwa tsakanin sojoji, ’yan sanda, sauran hukumomin tsaro, da kuma dakarun sa-kai (ɓigilante).
A cewarsa, samamen ya fi mayar da hankali ne a dajin Malam, wanda ya hada jihohin Bauchi, Filato da Taraba. Ya kara da cewa an kashe daruruwan ’yan bindiga yayin farmakin, yayin da jiragen yaki guda hudu suka yi ruwan bama-bamai a maboyarsu, lamarin da ya tilasta wa da dama daga cikinsu tserewa.
Haka kuma, dakarun sun lalata sansanonin ’yan bindigar tare da kona babura masu yawa da suke amfani da su wajen kai hare-hare. Bugu da kari, an katse hanyoyin da suke bi wajen samun makamai da kayan masarufi, matakin da ake sa ran zai rage karfinsu.
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa gwamnati ta bayar da wata dama ta musamman ga ’yan bindigar da ke son ajiye makamansu su mika wuya domin a tantance su tare da gyara halayensu.
“Wannan ba afuwa ba ce, dama ce kawai muka ba su su fito su mika wuya domin a duba halayensu a karkashin kulawar gwamnati,” in ji shi.
Ya kara da cewa yawancin ’yan bindigar ba ’yan asalin Jihar Bauchi ba ne, yana mai cewa ana shirin samar da wurin da za a ajiye wadanda suka mika wuya tare da iyalansu kafin a dauki mataki na gaba.
Domin tabbatar da dorewar zaman lafiya, gwamnan ya sanar da shirin fara tattara bayanan sirri na mazauna yankunan da abin ya shafa ta hanyar amfani da fasahar zamani (biometric data), tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Bayanan ’Yan Kasa (NIMC).
Sauran matakan sun hada da sanya ido na musamman a kasuwanni, tashoshin mota da sauran wuraren taruwar jama’a, ɗaukar ƙarin dakarun sa-kai don taimaka wa jami’an tsaro, da kuma tabbatar da cewa babu wani daji ko wuri da zai zama mafakar masu laifi ba tare da kulawar jami’an tsaro ba.
A ƙarshe, Gwamna Bala Mohammed ya jinjina wa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan goyon bayan da yake bai wa harkar tsaro, tare da kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai domin gano bata-gari.
