Masu yi wa ƙasa hidima 500 na shirin karɓar horo a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

An turo sama da masu yi wa ƙasa hidima 500 Jihar Zamfara da suka fara karɓar hoto ƙarƙashin shirin hukumar kula da masu yiwa ƙasa hidima ta Kasa (NYSC) a hukumance a yau Juma’a don shekarar hidimar ‘A’ ta 2026.

Mai Shari’a Murtala Abdullahi, a ma’aikatar shari’a ta Jihar Zamfara ya jagoranci rantsar da masu yiwa ƙasa hidimar a sansanin horar da matasan da ke cibiyar horar da malamai ta UBEC, da ke Gusau.

Da yake bayani a buɗe horaswar, Gwamna Dauda Lawal wanda Sakataren Dindindin na ma’aikatar matasa da wasanni, Alhaji Nasiru Galadima Ƙaura ya wakilta, ya tabbatar wa membobin ƙungiyar cewa gwamnatin jihar za ta jajirce wajen kare lafiyarsu da tsaronsu a tsawon shekarar hidimarsu.

Ya bayyana tsarin yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin muhimmin shiri don inganta haɗin kan ƙasa, ci gaban matasa, da kuma hidimar al’umma.

Gwamna Lawal ya kuma tabbatar musu da cewa an sanya isassun matakan tsaro don tabbatar da tsaronsu a lokacin zamansu a jihar.

Tun da farko, Ko’odinetan NYSC na Jihar Zamfara, Malam Muhammad Lawan Ahmed, ya bayyana kwas din horaswar a matsayin tushen haɗakan matasa a shekarar hidimar ƙasar su.

Ya ce an tsara shirin ne don a sanya tarbiyya, jagoranci, kishin ƙasa, da kuma ruhin haɗin kan ƙasa a tsakanin mahalarta bautar Kasar.

Mai kula da shirin ya buƙaci membobin ƙungiyar da su bi ƙa’idodi na sansanin, su shiga cikin dukkan ayyuka, don samun nasarar da ake buƙata.

Ya kuma nuna godiya ga Gwamnatin Jihar Zamfara saboda ci gaba da goyon bayan shirin, musamman gyare-gyare da aka yi kwanan nan a sansanin.

Bikin rantsar da sabbin masu yiwa ƙasa hidimar ya samu halartar gwamnati da kwamandojin tsaro, ciki har da kwamishinan ‘yan sanda, CP Ahmad Bello.

By ukarofi