Daliban Bichi sun yaba wa ɗan majalisa Abubakar Kabir kan zuba jari a fannin ilimi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar ɗaliban ƙaramar Hukumar Bichi ta gudanar da babban taro a Sakatariyar ƙaramar Hukumar domin bayyana goyon bayanta ga ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Bichi, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar, bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa ilimi da tallafa wa ɗalibai a yankin.

A cikin wata sanarwa da Jami’ar Yaɗa Labarai ta ƙaramar Hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, ta fitar, Shugaban ƙungiyar ɗaliban Bichi, Kwamared Mu’azzam Kabiru Adamu, ya bayyana cewa ɗaliban yankin sun gamsu da irin ayyukan ci gaban ilimi da ɗan majalisar ke aiwatarwa, yana mai cewa lokaci ya yi da za su mayar masa da alherin da ya yi musu.

Ya ce tsawon shekaru shida da Alhaji Abubakar Kabir ya shafe yana wakiltar al’ummar Bichi, ya ɗauki nauyin karatun dubban ɗalibai a ciki da wajen Nijeriya ba tare da nuna bambanci ba, lamarin da ya taimaka wajen sauya rayuwar matasa da dama.

A cewarsa, kusan ɗalibai 50,000 ne suka amfana da biyan kuɗaɗen makaranta da sauran tallafin ilimi da ɗan majalisar ya samar tun bayan hawansa kan kujerar wakilci.

Kwamared Mu’azzam ya bayyana cewa wannan gagarumar gudummawa ta sanya ɗaliban yankin suka ɗauki Alhaji Abubakar Kabir a matsayin jagoran da ya ba ilimi muhimmanci fiye da komai.

“Wanda yake yi mana alheri shi ne namu. In Allah Ya yarda, ɗaliban ƙaramar Hukumar Bichi za su ba da cikakken goyon baya ga Mai Girma ɗan Majalisar Tarayya a zaɓe mai zuwa. Ba shi kaɗai ba, duk ‘yan takarar da ya nuna mana daga shugaban ƙasa, gwamna, sanata, ɗan majalisar tarayya da na jiha, su ne za mu mara wa baya,” inji Kwamared Mu’azzam.

Ya ƙara da cewa, a matsayinsa na shugaban ɗaliban da ke jagorantar dubban matasa a yankin, zai ci gaba da wayar da kan mambobinsu kan muhimmancin tallafa wa shugabannin da ke zuba jari a fannin ilimi.

Shi ma da yake jawabi, Shugaban ɗaliban da Alhaji Abubakar Kabir ke ɗaukar nauyin karatunsu a faɗin Nijeriya, Kwamared Abdul-Aziz Umar Lawan, ya ce manufar ɗan majalisar tun farko ita ce gina al’umma ta hanyar ilimi.

Ya bayyana cewa tallafin karatun da ake bai wa ɗalibai ya taimaka wajen rage yawan matasan da ke barin makaranta, tare da ba su damar samun ingantaccen ilimi da zai amfani kansu da al’umma baki ɗaya.

“Ba ilimi kaɗai ake koyarwa a makaranta ba. Ana koyar da tarbiyya da ɗabi’a. Abin da ake kira character and learning duk ana samun su ne a makaranta. Wannan shi ne hangen nesan da Mai Girma ɗan Majalisa yake da shi wajen saka hannun jari a ilimi,” inji Kwamared Abdul-Aziz.

A nata jawabin, ɗaya daga cikin ɗalibai mata da suka amfana da shirin tallafin karatu, Bilkisu Yusuf, ta ce mata ma suna cin gajiyar tallafin ilimi kamar yadda maza suke samu, lamarin da ya ƙara musu ƙarfin guiwar neman ilimi.

Ta ce, ilimin da suke samu zai taimaka wajen gina iyalai nagari da kuma ci gaban al’umma gaba ɗaya.

“Idan mace ta samu ilimi, za ta tabbatar ‘ya’yanta ma sun samu ilimi. Haka kuma za ta iya tarbiyantar da su yadda ya kamata. Ilimi shi ne ginshiƙin rayuwa mai ɗorewa,” inji Bilkisu Yusuf.

Kungiyar ta kuma yi kira ga sauran masu riƙe da muƙaman siyasa da su ƙara mayar da hankali wajen saka hannun jari a fannin ilimi, tana mai cewa hakan shi ne hanya mafi inganci ta gina matasa masu anfani ga al’umma da ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply