Dalilan da suka sabbaba samun ambaliya mafi muni cikin shekaru 30 a Maiduguri

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Aƙalla dubunnan mutane ne suka rasa matsugunansu bayan aukuwar wata ambaliyar ruwan sama da aka yi a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ɓallewar tafkin Alua da ke yankin ta tsawon mako guda ta taimaka wajen samun ambaliyar.

Wannan shi ne karo na biyu da aka samu ambaliya irin haka a Maiduguri tun a shekarar 1994 da aka samu wacce ta mamaye kusan rabin birnin.

Cikin wata sanarwa da Kwamishinan Labarai da Tsaron Cikin gida, Farfesa Usman Tar ya fitar a safiyar ranar Talata, ya yi kira da a gaggauta ficewa daga yankunan da lamarin ya shafa, ya na mai shawartar waɗanda ke kusa da babban rafi su ɗauki matakin kare kansu daga iftila’in.

Sannan, an samu dabbobin da suka fice daga gidan kiwon dabbobi na garin waɗanda kawo yanzu ba a san halin da suke ciki ba.

Ambaliyar ta mamaye manyan gadaje da hanyar gidan kiwon dabbobi inda ta nufi makarantar Kwalejin kiwon lafiya wanda ɗalibanta tuni suka garzaya makarantar ‘Nursing’.

Kawo yanzu, ana fargabar abin da ka iya biyowa baya sakamakon ficewa daga gidan zoo da dabbobi masu haɗari suka yi a yayin ambaliyar.

By Babaji