
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince a fara aikin bada lambar ta shekarar 2024 ga ƴan Nijeriya da abokananta da suka taimaka wajen samun ci gaba a ƙasar.
Ministan Ayyuka na Musamman da Harkokin Cikin Gwamnati, Zaphaniah Jisalo ya faɗi hakan a yayin wani zama da hukumar ma’aikata ta Ma’aikatar, a ranar Talata.
Ya ce, gwamnatin tarayya za kuma ta karrama ƴan Nijeriyar da suka taka rawar gani a ɓangarorinsu a yayin gudanar da ayyukansu.
Ministan ya bayyana cewa, babu wani kuɗi da za a biya don karɓar lambar yabo ta ƙasa, ya na mai kira ga al’umma da su ƙauracewa bada kuɗi saboda za a ba su shaidar karramawar.
Daga ƙarshe, ya yi kira ga ƴan ƙasa su kasance masu jiran kira da kuma gabatar da waɗanda ake ganin sun cancanci samun kyautar kan ci gaba da suka samar wa ƙasa da ƴaƴanta.
