
Daga BELLO A. BABAJI
An dakatar da Anthony Joshua daga wasan Boxing na kwanaki 28 bayan da Daniel Dubois ya doke shi.
Ɗan wasan, wanda ya zama zakara har sau biyu a gasar heavyweight ya sha kaye ne a hannun Dubois wanda ya doke shi a mataki na biyar a ranar Asabar a filin wasa na Wembley.
Sakamakon kayen ne hukumar kula da Boxing ta Turai ta dakatar da Joshua na tsawon kwanaki 28.
Wannan doka ce daga hukumar kan cewa duk ƴan Boxing na Turai da aka doke su a irin wannan matakin, to za a zartar da hukuncin dakatarwa akan mutum.
Kawo yanzu dai Joshua ya bayyana aniyarsa ta cigaba da fafatawa a Boxing bayan ya yi watsi da raɗeraɗin da ke cewa zai yi murabus daga wasan.
Wasa na gaba da ɗan wasan zai yi shine wanda za a yi watan Fabrairun shekara ta gaba.
