Zaki ya kashe mai kula da shi a gandun dajin Obasanjo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wani abin alhini ya auku a wani gandun daji na tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun inda wani zaki ya farmaki mai kula da shi, Babaji Daule.

Gandun wani sashi ne na wajen ajiyar littafai na Olusegun Obasanjo (OOPL).

Rahotonni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne a safiyar ranar Asabar, 29 ga watan Satumba inda babban jami’in tsaron wajen ya bada rahoton batun da misalin ƙarfe 7:40 na safe.

Bayanai sun tabbatar da cewa, mai kula da wajen bai rufe ɗakin ajiyar zakin ba ne yadda ya kamata yayin da ya ke ƙoƙarin ba shi abinci.

Sakacin ya sa zakin ya fito daga ɗakin tare da farmakar sa inda ya ji masa raunuka a wuya waɗanda suka yi sanadiyyar mutuwar sa.

Tuni aka garzaya da gawar mamacin zuwa wajen ajiyar gawa ta babban asibitin Ijaye, yayin da zakin kuma aka harbe shi.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Omolola Odutola ya tabbatar da aukuwar lamarin tare da cewa su na gudanar da bincike a kai don kauce wa faruwar irin haka a nan gaba.

By Babaji