Shahararren ɗan Boko Haram, Bochum Abacha ya miƙa kan sa ga jami’an MNJTF

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wata nasara da aka samu a ƙoƙarin yaƙi da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi ita ce, shahararren ɗan Boko Haram mai suna Bochu Abacha ya miƙa kan sa ga jami’an haɗaka na MNJTF a ƙaramar hukumar Kukawa ta Jihar Borno.

Abacha, wanda ya kan yi ayyukansa na ta’addanci ne a yankin Monguno-Baga ya ce ya yi hakan ne saboda ayyukan da MNJTF ke gudanarwa da kuma janyewa daga ra’ayin cigaba da tafiya da ƙungiyar.

Ya tsere ne daga sansanin Boko Haram na Mussaram tare da wata bindiga mai ƙirar AK47, da wasu makamai da albirusai da wayar salula da kuma kuɗi da adadinsa ya kai N32,500.

A yanzu haka ya na bai wa jami’an bayanai na sirri da za su taimaka musu wajen cigaba da daƙile ta’addanci a yankin.

A wani atisayen ne a Gubio jami’an suka yi nasarar kai farmaki ga wasu ayarin ƴan Boko Haram da dare akan hanyarsu ta kai wasu kayayyaki acikin motoci uku ƙirar Toyota.

A nan ne aka yi ba takashi da ya yi sanadiyyar mutuwar ɗan ta’adda ɗaya da kuma ƙwato kayayyakin.

By Babaji