Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Ambasada Alhaji Nafiu Nuhu, Shugaban ƙungiyar Gandun Albasa ‘general furniture’ ya bayyana cewa Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta ba su aikin gudanar da dubban kujeru na zaman ɗalibai da malamai da za a sa a dukkan makarantun jihar.
Ya ce, wannan gagarumin aiki da gwamnati ta ɗauko ya nuna jihar Kano tayi nasarar samun nagantaccen shugaba jajirtacce da zai tsaya ya dubi matsalolin al’umma ya share musu kuka wannan shine shugabanci nagari.
Ya ƙara da cewa, kwanakin baya ya ayyana dokar ta ɓaci akan ilimi duk wanda yake Kano zai ga irin dubban kujeru da Gwamnati tasa kafintoci suka yi da za’a raba makarantu a dukkan ƙananan hukumomi 44 wannan kuwa ya samo asali ne bisa koyi da gwamna yake da jagora injiniya Rabiu Musa Kwankwaso domin lokacin da yayi Gwamna ya jajirce wajen inganta ilimi.
Ya ce, babu wata gwamnati da aka yi a jihar Kano da ta samar da kujeru masu yawa a makarantu kamar wannan Gwamnati ta Abba Kabir Yusuf tayi alƙawarin kowace makaranta a Jihar Kano sai an cika ta da abin zama sai an nemi ɗalibi mai zama a ƙasa an rasa ga littattafai ana rabawa da kayan makaranta domin cigaban al’umma ya dogara ne ga ilimi.
Ambasada Nafiu ya ƙara da cewa ita wannan gwamnati tana kai kowane irin aiki ne ga ahalinta su kafintoci na jihar Kano taga sune ya cancanta a baiwa aikin yin kujerun aka basu wannan ya taimaka wajen rage zaman banza da rashin ciniki da sama da mutum 11,000 ne suke amfana da yin aikin.
Ambasada Alhaji Nafiu Nuhu shugaban ƙungiyar Kafintocin na Gandun Albasa ya ce yanzu an soma da yin kujeru sama da Dubu 50 kuma za a cigaba da yi har sai an wadata dukkan malarantu a jihar Kano da kujerun zama. ya kuma godewa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan dama da ya basu suna yi masa fatan nasara a dukkan abinda yasa a gaba.
