Dalilin rashin saukar farashin abinci duk da ƙarin amfanin gona – Kyari

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan Noma da Samar da Abinci, Abubakar Kyari, ya ce samar da abinci ya ƙaru a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, amma matsalolin sarrafa amfanin gona da rarraba shi na ci gaba da sanya farashin abinci ya yi tsada.

Kyari ya ce, gwamnati ta samu gagarumar nasara wajen ƙara yawan amfanin gona, inda farashin amfanin gona a wajen manoma ya ragu, amma masu saye har yanzu ba su amfana da cikakken sauƙin ba saboda matsalolin da ke tsakanin wurin da ake samar da abinci da kasuwa.

Ministan ya bayyana hakan ne a wata hira da kafar ARISE NEWS ranar Juma’a, yayin da yake amsa tambayoyi kan dalilin da ya sa sauye-sauyen da gwamnati ke yi a fannin noma ba su yi tasiri sosai wajen rage farashin abinci ba.

“Mu koma baya mu duba alƙaluman shekarar 2023 da 2024. Idan aka kwatanta su da abin da sauye-sauyen gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka haifar, muna kan turbar da ta dace,” inji Kyari.

Ya ce, bayanan gwamnati sun nuna cewa kuɗin samar da amfanin gona a wajen manoma ya ragu, amma har yanzu ana fuskantar matsala wajen sarrafa amfanin gona. “Idan ka duba alƙaluman Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS), za ka ga cewa farashin sarrafa amfanin gona bai ragu ba, yayin da farashin samarwa ya ragu. Wannan na nufin farashi a wajen manoma ya ragu sosai. Don haka, akwai wasu gibi da ake buƙatar duba su. Amma mun magance matsalar samar da abinci, kuma mun samu gagarumar nasara a wannan fanni,” inji ministan.

Kyari ya danganta ci gaba da dogaro da Nijeriya ke yi da shigo da abinci daga ƙasashen waje da ƙaruwar yawan jama’a, ƙarancin yawan amfanin gona, matsalar samun filayen noma da tsadar kayan aikin noma da kuɗin samarwa.

Ya ce Nijeriya na ƙaruwa da mutane kusan miliyan takwas zuwa tara a kowace shekara, lamarin da ke sa samar da abinci ya kasance babban ƙalubale. “Saboda wasu dalilai, ba mu iya tafiya daidai da saurin ƙaruwar yawan jama’a ba. A matsakaici, muna ƙaruwa da mutane miliyan takwas zuwa tara a kowace shekara. Shekaru 25 da suka wuce, adadinmu ya kai kusan rabin abin da yake a yau, kuma bayan shekaru 25 masu zuwa, zai ninka abin da yake yanzu. Akwai kuma wasu abubuwa kamar samun filayen noma, yayin da yawan amfanin gona har yanzu yake a matakin da bai gamsar ba,” inji shi.

Ministan ya ce, domin magance wannan matsala, gwamnati na mai da hankali kan ƙara yawan amfanin gona, samar da ingantattun iri da kuma bai wa manoma kayan aikin noma da tallafi. Ya ce, gwamnati ta riga ta taimaka wa manoma da dama ta hanyar samar musu da kayan noma da iri cikin farashi mai rahusa.

Kyari ya ce gwamnati na ƙoƙarin rage dogaro da Nijeriya ke yi da shigo da sarrafa abinci daga ƙasashen waje ta hanyar amfani da injuna wajen noma, ƙara sarrafa amfanin gona a cikin gida da kuma kafa Yankunan Musamman na Sarrafa Amfanin Noma (SAPZ).

Ya ce, ana sa ran alƙaluman noman damina za su nuna gagarumar raguwar shigo da abinci daga ƙasashen waje. “Idan ka duba shigo da abinci, abin da ke ƙaruwa a alƙaluman shi ne abincin da aka sarrafa, yayin da amfanin gona da ake samarwa a gonaki ke ci gaba da raguwa wajen buƙatar shigo da shi,” inji shi.

Ministan ya ce, gwamnati na ƙoƙarin hana fitar da wasu kayan amfanin gona da ake samarwa a cikin gida, domin a sarrafa su a Nijeriya tare da ƙara musu daraja. Ya kuma ce dukkanin Yankunan Musamman na Sarrafa Amfanin Noma guda takwas da ake shirin kafawa za su fara aiki kafin ƙarshen shekara mai zuwa, yayin da gwamnati ta fara shirin mataki na biyu, wanda zai shafi kashi na farko na wasu jihohi 10.

A cewarsa, SAPZ zai mayar da hankali kan samar da amfanin gona, tattarawa, adanawa, sarrafawa da tallata shi. Ya ce, wannan tsarin zai taimaka wajen rage dogaron Nijeriya da abincin da aka sarrafa daga ƙasashen waje. Kyari ya kuma ce ingantuwar tsaro ta ba manoma damar komawa wasu gonaki da a baya suka kasa kaiwa saboda rashin tsaro.

“A shekarar 2023, gonaki da dama ba a iya zuwa gare su ba, amma yanzu an samu damar shiga cikinsu. A shekarar 2024 an samu girbin amfanin gona mai yawa, sannan a 2025 ma abin ya fi na 2024. Yanzu muna jiran alkaluman 2026 su fito. Wannan na nuna cewa an samu ƙarin damar zuwa gonakin da a baya suke cikin wuraren da rashin tsaro ya yi ƙamari,” inji shi.

Ya ce, gwamnati da rundunonin tsaro na ci gaba da ƙoƙarin dawo da waɗannan gonaki ƙarƙashin cikakken iko domin manoma su samu damar noma ba tare da fargaba ba. Ministan ya ce, ana sa ran fitar da alƙaluman samar da amfanin gona na shekarar 2026 tsakanin Oktoba da Nuwamba. Ya bayyana cewa National Agricultural Eɗtension Research Liaison Services (NAERLS), wadda ke aiki tare da Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci ta Tarayya da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ce ke samar da alkaluman noma a ƙarshen damina.

Sai dai ya ce gwamnati ta kuma umarci hukumar da ta riƙa fitar da alkaluman bayan kowane zagayen girbi, domin ƙarfafa noman duk shekara. A cewarsa, ana sa ran samun alkaluman zagayen farko na noman rani a watan Maris, yayin da za a fitar da na zagaye na biyu a watan Yuni.

By ukarofi

Leave a Reply