CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya rage Adadin Ruwan Manufar Kuɗi (MPR) daga kashi 26.50 zuwa kashi 23 cikin 100.

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Talata, 22 ga Satumba, 2026.

Cardoso ya ce Kwamitin Manufofin Kuɗi (MPC) na babban bankin ne ya amince da rage MPR zuwa kashi 23 cikin 100 a taronsa na 307.

Ya ƙara da cewa, an sake tsara tazarar cibiyoyin ba da rancen gaggawa (Standing Facilities Corridor) zuwa maki 50 sama da MPR da maki 300 ƙasa da MPR.

Haka kuma, ya ce an ci gaba da riƙe Adadin Kuɗin Ajiyar Tilas (Cash Reserve Reƙuirement – CRR) da kashi 45 cikin 100 ga bankunan ajiya, kashi 16 cikin 100 ga bankunan kasuwanci na musamman (Merchant Banks), yayin da aka bar shi a kashi 75 cikin 100 kan ajiyar kuɗaɗen ɓangaren gwamnati da ba sa ƙarƙashin Asusun TSA.

By ukarofi

Leave a Reply