Dandalin shawara: Ki taimaka min da bayani kan ‘khul’i’

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Assalamu alaikum. An wuni lafiya, ya aiki. Wata baiwar Allah ce ta ke neman shawara. Mijina ba mutumin arziki ba ne, ya kasance mai yawan musgunawa iyalinshi, ba ci, ba sha, bare sutura ga kuma neman mata, wallahi ko ɓoyo na ganin ido ba ya yi min.

An kai shekara uku rabon da ya ba ni kuɗi wai da sunan cefane a ci abinci a gidansa. Komai ni nake yi wa ‘ya’yana, har makaranta ma da taimakon wata baiwar Allah mai bada tallafi ta sa su, ni sai na ji da kuɗin tafiyarsu da abinci.

Ni dai kam ba zan ce ma ki na san daɗin aure ba, amfani ɗaya aure ya yi min shi ne, samun ‘ya’ya, ko shi kuwa kawai Allah ya ƙaddaro ne, don sai mu yi wata shida bai neme ni ba, sai ran da ya bushi iska zai kusance ne, kuma da ya gama ba ruwansa da tawa buƙatar. Na yi kai ƙara, na yi roƙo, amma shiru ka ke ji.

Shi ne fa na kai maƙura, na nemi ya sawwaqe min ko na huta. To sai ya je ya ɗauko wani malami wai ya gaya min abinda Allah Ya ce idan mace ta nemi saki, shi ne fa ya kira wata kalma wai ita ‘khulu’i’, ya yi bayanin kan wai idan Ina son mijina ya sawwaƙe min, to zan ba shi kuɗin sadaki, kuɗin da zai yi hidimar biki, da kuɗin da zai kama hayar inda zai sa matar ko na shekara biyu ne.

Aka yi lissafin kuɗi zunzurutu har dubu ɗari uku da arba’in. Wai su ne kuɗin da zan biya in fitar da kaina daga zaluncin mijina. Kuɗin da ko a ido ban taɓa ganinsu ba.

Shi ne na ce bari na aiko da tambayata gare ki, duk da na san ba za ki tuna ni ba, amma Ina ɗaya daga cikin masoyanki da suka yi kiranki a shekarun baya su na gaishe ki. Don Allah Ina son ƙarin bayani kan wannan ‘khulu’i’ da suka ce, da kuma tambayar ko akwai wani sasauci da Musulunci ya yi wa irinmu marasa ƙarfi, waɗanda azaba ta sa su neman rabuwa ba son zuciya ba. A gaida yara. Na gode.

AMSA:

Wa’alaiki salam wa rahmatullah. Bari mu soma da bayanin ma’anar khul’i kafin mu ji vangaren da Musulunci ya ajiye ki a wannan lamari. Khul’i hukunci ne na fansar kai da mace zata iya yi a yayin da ta yi sha’awar rabuwa da mijinta.

Kamar yadda ki ka sani, hukuncin tsinke igiyar aure na ɗaya daga cikin iko da Musulunci ya ba wa miji, hakan na nufin ba mai ikon sakin mace a take, kuma ta saku, sai mijinta, sai kuma wasu dalilai da suka ba wa alƙali damar iya raba auren.

Da wannan ne Musulunci ya yi tanadi ga mata, kasancewar sa addinin adalci, tunda bai bata ikon sakin mijinta idan ta yi muradin hakan, sai ya fito da hanyar da zata zama mafita gare ta yayin da buƙatar rabuwa ta taso ta vangaren ta, wato ta fanshi kanta daga wurin mijinta da ke da ikon sakinta, ta hanyar ba shi wani abu daga dukiya don ya samu damar yin wani aure cikin sauƙi.

Kamar yadda aya a cikin littafi mai tsarki ta faɗa a cikin suratul Baƙara, aya ta 229, inda Allah Maɗaukakin sarki ya ce, “Saki sau biyu yake, sai a riqe shi da alkhairi, ko kuwa a sallama bisa kyautatawa. Kuma ba ya halatta a gare ku (maza) ku karve wani abu daga abin da ku ka ba su, face fa idan su (ma´auran) na tsoron ba za su tsayar da iyakokin Allah ba.

Idan kun (danginsu) ji tsoron ba za su tsayar da iyakokin Allah ba, to, babu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Waɗancan iyakokin Allah ne saboda haka kada ku ƙetare su. Kuma wanda ya ƙetare iyakokin Allah, to waɗannan su ne azzalumai.”

Idan mun ɗauki kusa da ƙarshen ayar, inda Allah ke cewa, “idan kun ji tsoron ba za su tsayar da iyakokin Allah ba, to babu laifi a kansu cikin abin da ta yi fansa da shi.” A daidai nan ne khul’i ya samu muhallinsa a addini, kuma ya samu halaccin sa.

Waɗanne dalilai ne ke sa a yi khul’i?

Yayin da mace ta ji ta tsani zama da mijinta, ta dalilin an wayi gari ta daina jin sonsa a ranta, ko ta gaji da auren bisa wani dalili na ra’ayin kanta, amma mai ƙwari, kuma tana tsoron saɓa wa Allah idan ta ci gaba da zama da mijin dalilin rashin son zaman da take, ta hanyar bijirewa buƙatarsa ko kasa yi masa biyayya.

Ta yaya ake yin khul’i?

Hanyoyi biyu ne za a iya gina khul’i a kansu, wanda ya danganta da irin zaman da mace ke yi da mijinta. A wani lokaci, za a iya tarar da cewa, zaman lafiya ake yi tsakanin mace da mijin, sai dai rashin so ko wani dalili da ta ɗauka da muhimmanci ne kawai ke yi mata shamaki da jin daɗin zama da mijin nata. A irin wannan za su iya yin yarjejeniya tsakaninsu.

Cikin ruwan sanyi ta yi masa bayanin buƙatarta, da kuma neman fansar kanta da take yi daga aurensa. A nan za su iya tsayar da matsaya, na abinda zata ba shi a matsayin kuɗin raba aurensu. Idan har sun yi matsaya, sai su sanya shedu na daga dangi don samun tabbaci.

Hanya ta biyu ita ce ta wurin shari’a, ko malamin da ya saba yin hukuncin da ya danganci aure, hakan na samuwa idan abin na neman zama na fitina, ko mijin ya ɗauki abin da zafi, ko kuma dama ba zaman lafiya ake yi ba. Alƙalin da ta kai ƙara wurin sa, ko malamin shi zai nemo mijin, ya shiga tsakani har a kai ga matsaya.

Menene hukuncin mace ta nemi khul’i?

Za mu ci gaba a mako mai zuwa.