Daga BASHIR ISAH
Allah ya yi wa darakta a Kannywood, Aminu Surajo Bono, rasuwa a yammacin Litinin, 20 ga Nuwamba, 2023, bayan da ya yanke jiki ya faɗi.
Da safiyar Talata, 21 ga Nuwamba, ake sa ran za a yi jana’izar marigayin a Kano.
Wannan rashi ya kaɗa ‘yan fim su da sauran jama’a ainun, musamman ganin yadda rasuwar tasa ta yi ba-zata, ba ciwo ba ko hatsari.
Marigayi Aminu yana daga cikin daraktocin da tauraronsu ke haskawa, musamman a ɓangaren bada umarnin shirya waƙa.
Ya yi firamare da sakandire a Kano, sannan ya fara fim a shekarar 1999.
