Dattawan Arewa sun bayyana Marigayi Bashir Tofa a matsayin mai kare al’umma

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ranar Larabar da ta gabata ne Ƙungiyar Dattawan Arewa suka kai ziyarar ta’aziyya ga gwamnatin Jihar Kano kan rasuwar Alhaji Bashir Othman Tofa da wasu manyan mutane ‘yan Jihar Kano.

Da yake jagorantar tafiyar, shugaban ƙungiyar dattawan, Farfesa Ango Abdullahi wanda ya samu wakilcin Wazirin Bauchi Alh. Muhammad Bello Kirfi ya ce sun je gidan gwamnatin jihar Kano ne domin yin ta’aziyyar dattijo mai faɗa-a-ji a jihar, Bashir Tofa wanda ya rasu ranar Litinin da safe.

“Mun zo ne don mu yi muku ta’aziyyar rasuwar Sarkin Bai, Alhaji Mukhtar Adnan wanda mutum ne mai mutumci, ƙwararren likita wanda ya bada gudunmuwa sosai da kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka samar da ƙungiyarmu Dr. Ibrahim Datti Ahmad da kuma rasuwar gogaggen ɗan siyasa, Alh. Bashir Othman Tofa.

“Sarkin Bai uba ne a gare mu, Dr. Ibrahim Datti Ahmad shi kuma mutum ne jajirtacce a dukkan lamuranmu, shi kuwa Bashir Tofa mutum ne wanda ya tsayu akan kare mutunci kansa da al’ummar jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.

“Waɗannan mutane masu daraja sun bayar da gagarumar gudunmuwa wajen ci gaban arewacin Nijeriya da ƙasa baki ɗaya,” ya ce.

Ya ƙara da cewa, suna alhinin rashin waɗannan manyan mutane waɗanda suka bada gudunmuwa musamman ta fuskar ci gaban al’umma.

“Za mu ci gaba da yi musu addu’a Allah ya jiƙansu da rahama, kuma ya sa kyakkyawan ayyukan su a mizani. Ya yi musu sakayya da gidan Aljanna Firdausi. Ya kuma ba Jihar Kano da iyalansu haƙurin wannan rashi,” inji shi.

Farfesa Ango Abdullahi ya kuma nuna farin cikinsa bisa kyakkyawar tarbar da gwamnatin jihar Kano ta yi musu.

Da yake mayar da jawabinsa, Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umaf Ganduje wanda mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta, ya nuna farin cikin sa da ziyarar da ƙungiyar dattawan ta kawo musu don jajantawa gwamnatin jihar da kuma al’ummar jihar Kano a daidai lokacin da suke alhinin rashe-rashen.

“Haƙiƙa mun rasa masu faɗa-a-ji waɗanda suka tsaya tsayin daka wajen bada gudunmuwa da ci gaban Jihar Kano. Mu na musu addu’a da fatan dacewa a ranar gobe ƙiyama,” ya ce.