Haramta amfani da gawayi a Jihar Nasarawa ya fara janyo guna-guni

Daga IBRAHIM HAMZA MUHAMMAD a Lafia

A kwanakin baya ne Gwamnatin Jihar Nasarawa ta haramta yin tu’ammali ko kuma sarrafawa, saye, sayarwa ko yin amfani da gawayi a matsayin makamashi a jihar bakiɗaya.

Babban Sakatare a Ma’aikatar Muhalli da Albarkatun Ƙasa, Alhaji Aliyu Agwai, ne ya bayyana haka garin Lafiya, babban birnin jihar, inda ya ce daga yanzu haramun ne sarrafawa da saye da sayarwa da kuma yin amfani da gawayi a jihar.

A cewarsa, yadda ake samar da gawayi yana tattare da illoli da dama ga muhalli, gurɓata yanayi da kuma ƙara zafafa yanayi.

Babban Sakataren ya ƙara da cewa, ƙona itatuwa domin samar da gawayi da yin amfani da shi yana da illoli da dama da ake ƙoƙarin ragewa, inda ya bayyana cewa, “sare itatuwa yana haifar da rashin ingantaccen muhalli ga dabbobi wanda bai dace ba.”

Sannan ya ƙara da cewa, “kusan dukkan dabbobin da ke kan doron ƙasa da tsirrai sun dogara ne da dazuzzuka, kuma akasarinsu ba za su rayu ba sai idan sun rasa muhallansu.”

A ƙarshe, ya gargaɗi masu ciniki da yin amfani da gawayi da su bari, don duk wanda aka kama, za a hukunta shi ko ita.

Amma binciken da Blueprint Manhaja ta gudanar ya nuna cewa, akwai manyan ƙalubale dangane da wannan ƙuduri na gwamnati.

Wani magidanci mai suna Malam Shehu Ɗanladi ya ce: “ta yaya za a hana amfani da gawayi bayan gas na girki da kananzir ba su wadata ba? Sannan inda aka same su, to suna da tsada matuqa ga mai ƙaramin ƙarfi.

“Tulun gas mai kilo 12 dai ya kama ne daga Naira 10,000 zuwa sama, rishon kananzir ya kama daga Naira 4,000 zuwa sama.”

Sannan ya qara da cewa, “shi kuma murhun gawayi ya kama daga Naira 1,000 zuwa 2,000. Sannan kuma ko gwangwani mutum ya fafe, zai iya ɗora masa gawayi ya biya buƙata.”

Wata mata ta ce, ya kamata a samar da tsarin aiwatar da shirin samar da makwafin gawayi zuwa gas da kananzir cikin sauƙi a shekarun biyar kafin a zartar da shirin hukunta masu karya dokar.

Wata majiya daga Rundunar ‘Yan Sanda da sauran hukumomin tsaro da sauransu a jihar sun nuna a fili ɓaro-ɓaro cewa, ba su da ƙarfi da yawan jami’an da za su iya aiwatar da dokar bincikowa da kamawa da gurfanar da waɗanda suke mu’ammala da harkar gawayi. Dalilan a cewarsu sun haɗa da rashin yawan ma’aikata da rashin motocin aiki, ga kuma girman da jihar ta ke da shi.

Tun a shekarun baya, ma’aikatar take ta kai gwauro da mari, don ƙoƙarin ganin an hana harkar gawayi, amma sai a yanzu abin ɓoye ya fito fili.

Blueprint Manhaja za ta sanya ido domin ganin an aiwatar da wannan shirin kai da ƙafa, ko kuma wani shirin kawai na jeka-na-yi-ka, don burge ƙudurin ƙasashen Yamma da Majalisar Ɗinkin Duniya.

A ƙasashen da aka ci gaba, an samar da wadataccen gas na girki kafin a hana sare bishiyoyi da samar da gawayi. Amma a wannan yanki na duniya, muna son mu aiwatar da dokar bayan gas na girki, bai wadata ba sam.