Yadda aka gudanar da bikin aure da ƙaddamar da littafin Editan Blueprint Manhaja a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano 

A Asabar ɗin da ta  gabata, 25 ga Disamba, 2021, ne aka ɗaura aure tare da ƙaddamar da littafi mai suna Ruwan Jakara, wanda marubuci kuma Editan jaridar Blueprint Manhaja, wato Nasir Sa’ad Gwamgwazo, ya rubuta.

An dai ɗaura auren ne a Masallacin Wudilawa da ke kusa da gidan Sarkin Kano, daura da Gidan Makama, yayin da aka yi walima da ƙaddamar da littafin a babban ɗakin taro na Kannywood TV da ke unguwar Tudun Yola kusa da Ƙofar Kabuga akan hanyar zuwa Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke cikin birnin Kano.

Tun da farko a jawabinsa, marubuci kuma jarumi kuma mai shirya finafinai a masana’artar Kannywood, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, gwamnan fim ɗin Kwana Casa’in, ya yi bayani a kan muhimmancin Rubutu da Fim, inda ya ce, “malamai sai su yi shekara da shekaru su na wa’azi, amma ba a saurare su ba, amma ɗan fim guda ɗaya idan ya yi magana sai a saurare shi kuma a bi shi,” don haka ya ce, tasirin fim ya na da matuƙar yawa. 

“Amma duk da wannan, ya mu ke ɗaukar kanmu? Shin mu na wakilcin al’adunmu da ɗabi’unmu da harshenmu da mutanenmu a lokacin da mu ke gabatar da ayyukanmu? Idan ɓera da sata, to daddawa ma da wari. Don haka akwai buƙatar mu sanya kishin al’ummarmu da mutunta al’adar mu a harkarmu ta rubutu da ta fim,” inji Gidan Dabino.

A jawabinsa, Dr. Ahmad M. Sarari, wanda shi ne shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), ya ce, Nasir Gwangwazo mutum ne mai hikima da basira. 

Ya ci gaba da cewa, “a shekara ta 2002 a ƙasar Faransa an yi kwana 10 ana haska finafinai daga ƙasashe daban-daban, amma da aka zo fim ɗin Waraka, wanda Nasir Gwangwazo ya rubuta, sai ga shi Turawa suna kuka suna zubar da hawaye a kan fim ɗin, kuma kuɗi kaɗan aka kashe wa fim ɗin, amma a gurin akwai finafinan da aka kashe wa Dala miliyan 10 zuwa 20, amma da ya ke an rubuta kyakkyawan labari a Waraka, hakan ya sa Turawa suna kuka suna share hawaye lokacin kallon sa, wanda kafin mu fito daga inda ake nunawa mutane sun yi layi suna jiran su sayi fim ɗin.”

Sannan ya yi jinjina da yabo ga Nasir S. Gwangwazo akan buga wannan littafi da raba shi ga al’umma a kyauta.

Shi ma a jawabinsa na gabatar da littafin, malami a jami’ar Bayero ta Kano mai ɗauke da farfesa biyu a kansa kuma tsohon shugaban Jami’ar NOUN, wato Farfesa Abdullah Uba Adamu, ya ce, Nasir Gwangwazo ya yi wani abu wanda shi dai a cikin shekaru 65 na rayuwarsa a Kano bai taɓa ganin wani ya yi ba.

“An yi biki, an zauna an ci abinci, an ƙaddamar da littafi a lokacin da aka kammala cin abinci. Wannan shi ne na farko a tarihi. Wannan ya nuna cewa, Nasir Gwangwazo ya na da kishin jama’a. Allah ya ba shi basira kuma ya ke ganin cewa, wannan basira ya kamata al’umma su amfana da ita. Idan da wani ne, ba zai yi ba, don kar wasu su amfana, amma shi ya yi, kuma aka raba kyauta. Don haka wannan babbar gudunmawa ce ga mutane masu sha’awar yin rubutu da masu son kaifafa basirarsu.”

Babban Editan Jaridar Blueprint Manhaja Nasir Sa’ad Gwangwazo ya bayyana jin daɗinsa ga waɗanda suka halarci ɗaurin aurensa da ƙaddamar da littafin, inda ya ce, “Ina yin rubutu ne, don sha’awa, ba don samun kuɗi ba. Don haka idan Allah ya hore min kuɗi da zan buga littafi kyauta, to haka ne burina a kodaysushe, ba wai don na samu kuɗi ba.” 

Gwangwazo ya ƙara da cewa, “maimakon na yi biki a kama Event Centre a yi rawa a yi kiɗa a yi liƙi, shikenan abu ya wuce, shi ya sa na ce, gara na ƙaddamar da wani abu na ilimi, wanda wataƙila wasu za su amfana har abada. Ka ga kenan ba biki kawai aka yi ba, an yi wani abu ne da zai amfani al’umma.”

Sannan ya yi kira ga sabbin marubuta da su nemi wannan littafi su karanta, domin su ga yadda ake tsara labarin fim. “Kuma Ina shawartar marubuta a kan lallai su yi bincike kafin su yi rubutu, domin hakan zai taimaka wa marubuci ya yi rubutu mai ma’ana da tasiri a cikin al’umma,” inji shi.

Malam Nasir Gwangwazo dai ya rubuta finafinan Hausa fiye da guda 43, yayin da ya fitar da littafi guda ɗaya, sannan ya rubuta wasan kwaikwayo na radiyo aƙalla guda 3 masu dogon zango. Bugu da ƙari, ya shirya finafinai da dama.

Taron dai ya samu halartar manyan marubuta da ‘yan jarida da ‘yan fim da suka haɗa da: Gwarzon marubuci kuma ɗan fim Malam Sunusi Shehu Daneji, wanda shi ne ya ƙirƙiri sunan Kannywood a 1999 da marubuci kuma darakta a masanaartar Kannywood Bala Anas Babinlata da Darakta Aminu Saira da Ali Nuhu da mai shiryawa Abdul Amart.

Akwai Shugaban tashar talabijin ta Farin Wata da Vision FM, Malam Umar Farouk Musa, da fitaccen ɗan jarida kuma tsohon Shugaban Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), Malam Nasir Zaharaddin, da marubuciya kuma malamar Jami’a (Dr) Bilkisu Yusuf Ali da Marubuciya Fauziyya D. Sulaiman da shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Ƙasa (ANA) Reshen Kano, Malam Tijjani Muhd. Musa, da Malam Umar Gombe, shugaban riƙo na MOPPAN reshen Jihar Kano da ‘yan jarida Amina Yusuf Ali da Al’amin Ciroma da Marubuciya Hauwa Mai Turare (Ƙamshi) da fitaccen mawaƙi, Nazifi Asnanic, tare da ’yan uwa da abokan arziki da dama daga sassa daban-daban na Nijeriya.