Babu maganar komawata APC – Kwankwaso

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ba shi da wani shiri na barin jam’iyyar sa ta PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya.

Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne cikin wata hira da ya yi da gidan rediyon DW da ke ƙasar Jamus.

DW ya rawaito Sanata Kwankwaso ya na cewa a yanzu dai ba shi da wata niyya ta barin jam’iyyar PDP zuwa APC, kamar yadda a ke ta jita-jitar zai bar jam’iyyar saboda rashin jituwar da ba a yi da shi a jam’iyyar.

“Maganar sauya sheqa babu ita a yanzu ɗin nan. Ba na magana da wasu mutane kan cewar zan koma APC,” inji Kwankwaso.

Jita-jita ta yi ƙarfi cewa Kwankwaso zai sauya sheƙa zuwa APC, kuma zai sulhunta da abokin burminsa a siyasa, Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje bayan da gwamnan ya kai masa ziyarar ta’aziyyar rasuwar ƙanin sa, Inuwa Kwankwaso.

Sai dai kuma a ƙarshen makon da ya gabata, sai gwamnatin Ganduje ta yi wa Kwankwason raddi kan kalaman da ya yi cewa gwamnan bai ci zave ba a shekarar 2019.

Idan za a iya tunawa an fara raɗe-raɗin Kwankwaso da Ganduje za su yi sulhu ne tun bayan da Gwamna Ganduje ya kai wa Sanata Kwankwason ziyarar ta’aziyyar ƙaninsa da ya rasu a kwanakin baya.