Korona: Kashi 60 za a bari su shiga kallon gasar Kofin Afrika

Daga WAKILINMU

A tsakanin watannin Yuni da Yulin bara ya kamata a yi gasar, amma annobar Korona ta sa aka ɗage zuwa bana.

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta nahiyar Afirka CAF ta ce kashi 60 zuwa 80 na ’yan kallo za a bari su shiga filayen wasanni da za a kara gasar cin kofin nahiyar na AFCON.

Matakin a cewar hukumar na da nasaba da annobar COVID-19.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, CAF ta ce bayan wata tattaunawa da ta yi da hukumomin cikin gida na Kamaru, sun cimma matsaya akan cewa kowanne filin wasa za a bar ‘yan kallo kashi 60 ne zuwa 80 su shiga kallo.

A ranar 9 ga watan nan na Janairu za a buɗe gasar ta cin kofin nahiyar Afirka, wacce Kamaru ke karɓar baƙunci.

Za kuma a kammala a ranar 6 ga watan Fabrairu kamar yadda jadawali gasar ya nuna.

A tsakanin watannin Yuni da Yulin bara ya kamata a yi gasar, amma annobar COVID ta sa aka xage zuwa bana.

Qasar Aljeriya ce ke riqe da kofin gasar.