Dogara Yaro ne Sarkin Hausawan Legas – Tinubu

Daga WAKILINMU

Ɗan takarar Jam’iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas, Sanata Ahmed Bola Tinubu, ya amince da Alhaji Aminu Dogara a matsayin Sarkin Hausawan Jihar Legas, lamarin da ya warware matsalar shugabanci da ta kunno kai kuma ta dabaibaye al’ummar Arewa mazauna Birnin Ikko, wato Legas.

Asiwaju Bola Tinubu ya kawo ƙarshen rikicin ne a ranar Juma’a, 18 ga Nuwamba, 2022, bayan da ya amince da rahoton kwamitin da ya kafa ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da Alhaji Lawal Abbas Garba a matsayin Sakataren Kwamitin.

A yanzu an amince da Alhaji Aminu Dogara Yaro a matsayin Sarkin Hausawan Jihar Legas, yayin da Dr. Mohammad Banbado zai cigaba da kasancewa Sarkin Fulanin Legas.

Bugu da ƙari, ɗan takarar Shugaban Ƙasa na APC ya amince da Sa’adu Yusuf Gulma a matsayin Shugaban Al’ummar Arewa na Jam’iyyar APC a jihar ta Legas.

Idan za a iya tunawa, Tinubu ya naɗa kwamitin haɗaka ne bisa damuwarsa da yadda rikicin shugabanci ya kunno kai tsakanin al’ummomin Arewa mazauna Jihar Legas, inda a jiya ya amince da rahoton kwamitin bayan ya karɓe shi daga hannun shugabannin kwamitin.