Sharhin littafin ‘Katsina Gidan Dallaje: Tarihin Malam Ummarun Dallaje’

Daga DANJUMA KATSINA

Sunan littafi: Katsina Gidan Dallaje: Tarihin Malam Ummarun Dallaje
Marubutan littafi: Sulaiman Yusuf Safana, Lawal Rufai Safana, Muhammad Bello 
Yawan shafuka: 194
Shekarar bugawa: Nuwamba, 2021
Mai sharhi: Danjuma Katsina

A karon farko an buga littafin zuriyar Dallazawa, wanda Dallazawa suka rubuta da kansu. Marubutan sun yi amfani da rubutu da kuma rahotanni da aka taskace na tarihi. Kafin fitowar wannan littafin, tarihin ana samun shi ne gutsutstsure a littafan tarihi daban-daban. Wasu bayanan kuma ana samun su a rahotannin turawan mulkin mallaka.

A karon farko wasu ‘yan zuriyar Dallazawa sun xau lokaci suna bin littafan da aka kawo tarihin Dallazawa da wasu littafan da malaman jihadi suka rubuta, suka kawo bayanan Dallazawa da kuma Rahotanni da Turawan mulkin mallaka suka rubuta, suka yi nazarin su, kuma suka tsamo bayanan inganattattu, suka rubuta littafin na ‘Katsina Gidan Dallaje’, tarihin zuriyar malam ummarun Dallaje’, (Dallazawa 1700 zuwa 1982). Dakta Aliyu muri na Sashen Nazarin Tarihi a jami ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina, shi ne malamin tarihi da ya yi editin na aikin kafin a buga shi Inda ya tabbatar duk bayanan da aka kawo sun cika mizanin tarihi.
Littafin ya kawo cikakkiyar wasiƙar ‘Usul Al- siyasa’. wasiƙa wadda Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya rubuta wa Malam Ummarun Dallaje akan ƙa’idojin shugabanci. Wannan shi ne karon farfko da aka fassara wasiƙar zuwa harshen Hausa. Wasiƙa ce mai cike da ilimi, wanda a wannan lokacin da ake, lokacin dimokuraɗiyyar da zaven shugabanni ya kamata duk wani mai neman takara ko wanda ke bisa muqami ya karanta ta.

Littafin ya zo da wasu hotunan tarihi masu ma’ana da kuma tuna baya akan tarihin Katsina da Gidan Sarautar Dallazawa. Wanda aka ciro su daga dubban hotuna wanda wani ɗan gidan zuriyar ya ɗau shekaru yana tarawa.
Littafin an rubuta shi da harshen Hausa, domin manufar ya shiga lungu da saƙo da kuma sauƙin karatu ga kowane ɓangare da neman sharhi ko bayani ba, wanda idan wani harshe aka rubuta shi wasu ne kawai zasu iya karanta shi. Sannan su fassara ma waɗansu.

Bayan sadaukarwa, ta’aliƙi da godiya, littafin yana da babi har guda huɗu. Babi na biyar kammalawa ne da kuma rataye. Kowane babi ya yi bayani filla-filla akan abin da aka gina babi akan shi. Bangon littafin zanen gidann sarki ne, yadda yake tun zamanin Dallazawa da kuma wani ɗauke da tuta bisa doki, bauyan littafin kuma hotuna ne da bayanan marubuta littafin.

Babi na farko na littafin taken shi, Zuriyar Dallazawa, a cikin jinsin Fulani, wanda suka kawo duk bayanan tarihi da aka kawo na asalin zuriyar Dallazawa. Da kuma tarihin asalin Fulani da suka tugo daga jinsin sahabin Manzon Allah [saw] mai suna ukuba ben Nafi, sannan suka kawo bayanan masana tarihi da rubutun da suka yi akan asalin Dallazawa. Da kuma yadda Dallazawa suka zo garin Dallaje. Da asalin na garin dallaje, duk a babi na ɗaya daga shafi na 1 zuwa na 12.

Babi na biyu wanda ya fara daga shafi na 13 ya ƙarƙare a shafi na 38 mai taken jihadin Shehu Usman Xan Fodiyo, yaƙe-yaƙen Mallam Ummarun Dallaje. Babin ya ɗauko tarihi tun kafin jihadin Ɗan Fodiyo da yadda suka haɗu da Malam Ummarun Dallaje, don neman ilimin addinin Musulunci. A wannan babin an kawo duk yaƙin da Malam Ummarun Dallaje ya halarta har zuwa amso tuta, don jihadi a Katsina. Har zuwa jihadin Katsina.

Babi na uku wanda ya fara daga shafi na 39 zuwa na 101 mai taken Kafuwar Daular Usmaniyya. Ya kawo bayanai da tarihin duk sarakun Dallazawa a Daular Musulunci. Wanda ya fara daga Mallam Ummarun Dallaje 1807 zuwa 1836. Sai Saddiku Ummarun Dallaje 1836 zuwa 1844, sai Muhammadu Bello Ummarun Dallaje 18441869, sai Ahmadu Rufai ɗan Ummarun Dallaje. 1869 zuwa 1870 sai Ibrahim ɗan Muhammadu Bello 1870 zuwa 1882. Sai Malam Musa ɗan Ummarun Dallaje 1882 zuwa 1887 . Bayan rasuwar Abubakar ɗan Sarki Ibrahim ya gaje shi wanda turawa suka iske a bisa kujerar sarautara Amiril Muminina.

A wannan babi marubutan sun yi ma tarihi adalci inda duk wata matsala da aka samu na gadon sarauta lokacin rasuwar kowane sarki sun kawo ta, kamar yadda tazo a tarihi duk matsalolin da Dallazawa suka fuskanta na yaƙe-yaƙe, zagon ƙasa da makida duk sun kawo. Hatta asalin farkon alaƙar Dallazawa da Sulluvawa sun kawo shi ne lokacin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Ɗan Ummarun Dallaje wanda ya jawo zuriyar Dahiru kakan Muhammadu Dikko cikin fadar Sarkin Katsina.

Babi na huɗu daga shafi na 101 zuwa na 164 shine babi mafi tsawo a littafin mai taken Sarakunan Katsina Lokacin Turawan Mulkin Mallaka. Littafin ya kawo tarihin yadda turawa suka shigo Katsina, suka iske Sarkin Katsina Abubakar yana sarauta. Rubutun ya kawo yadda Sarkin Katsina ya wakilta Muhammadu Dikko ya wakilce shi a wajen turawa.

Ya kuma bada tarihin sarakuna Dallazawa da turawa suka yi aiki da su. Na farko, Abubakar ɗan Ibrahim 1887 zuwa 1905, an kawo yadda aka cire shi daga mulki da yi masa gudun hijira, sai Malam Yaro ɗan Malam Musa 1905 zuwa 1906 shima an kawo hawan shi da yadda aka cire shi. Daga shafi 125 har zuwa 154 an kawo labarin rayuwar Dallazawa ne a zamanin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko. Daga shafi na 155 zuwa 164 an kawo yadda Usman Nagoggo ya zama sarki da irin rawar da yariman Katsina ya taka wajen dai dai ta biyayya ga sabon sarki. Da yadda zumunci ya ƙara kyautata tsakanin Dallazawa da Sulluvawa.

Babi na biyar daga shafi na 165 zuwa 170 nazari ne akan tarihin Katsina da ya kasu kasha uku, kafin jihadi, lokacin jihadi da zamanin turawa da abin da ya biyo bayan shi. Rataye na ɗaya bayanu ne akan sarautun da Dallazawa suke riƙe da ita ada, yanzu kuma bata a hannunsu. Rataye na biyu fassarar ‘Usul Siyasa’ ne cikakke. Rataye na uku jerin sunayen ‘ya’yan Ummarun Dallaje su 19.

A shafi na 193 zuwa na 194 jerin littafai na tarihi da bincike waɗanda aka dogara da su wajen nazari da binciken rubutun. An yi ma littafin bugu mai kyau da kuma tsanwar takarda. Littafin yazo dai dai lokacin buƙatar shi. Watau zamanin da aka samu wasu sheɗanu suna shiga yanar gizo suna sukar jihadin Shehu Usman Ɗan Fodiyo da kuma zuriyar Fulani bakiɗaya.