Matashin da zai buɗe karatun Alƙur’ani a gasar cin kofin duniya na yau

Daga IBRAHIM HAMISU

Wani matashin yaro mai buƙata ta musamman mai suna Ƙanim Al Miftah wanda mahaddacin Alƙur’ani ne shi ne zai buɗe gasar cin kofin duniya da karanta ayoyin Ƙur’ani mai tsarki a yau.

Za a dai a fara gasar Cin Kofin Duniya ne a yau Lahadi a ƙasar Qatar, da ƙarfe 5 na yamma, inda mai masaukin baƙi ƙasar Qatar za ta kara da ƙasar Danmark.