Nijeriya tana fuskantar mafi munin matsin tattalin arziki a tarihi – Rahoton bincike

Daga AMINA YUSUF ALI

A cikin watan Oktoba na bana dai matsin tattalin arzikin Nijeriya ya sake ƙaruwa da kaso 21.09.

Waɗannan alƙalumman sun kasance mafi munin halin matsin tattalin arzikin da ƙasar ta taɓa shiga a tarihi.

Wannan bayani dai ya samu ne daga sakamakon binciken ƙididdigar farashi ta (CPI) da hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) suka yi a cikin watan Oktoban 2022.

CPI ta auna kimar canjin kuɗaɗe a kan farashin kaya da ayyuka, inda ta gano sun yi gudun wuce sa’a har i zuwa ƙarin kaso 21.09 saɓanin yadda yake a kaso 20.77 a watan Satumban bana.

Rahoton na NBS ya bayyana cewa, idan za a bi ƙididdigar ƙaruwar matsin tattalin arzikin na wata-wata, za a samu akwai tazara sosai daga yadda kason yake a watan da ya gabaci Oktoban da kuma Oktoban kansa. Gwari-gwari dai za a ce an samu banbancin 0.11 a tsakaninsu.

Hakazalika kuma, idan aka ce za a kwatanta ƙaruwarsa a tsahon shekara wato watanni goma sha biyu. Rahoton CPI na Oktoban shekarar bara ta 2021 ya bayyana cewa, ƙaruwar matsin tattalin arzikin Nijeriya na wancan lokacin ya kasance kaso 16.96.

Amma a Oktoban 2022 kuma sai ya yi tashin gwauron zabon da ya zama mafi munin a tarihin tashin matsin tattalin arzikin ƙasar.