Dokar haraji za ta rushe TETFund, NASENI, NITDA  idan aka tabbatar da ita — Zulum

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Tallafin Ilimi na Manyan Makarantu (TETFund), Hukumar ƙasa ta Kimiyya da Injiniyanci (NASENI), da Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta ƙasa (NITDA) za su daina aiki idan har dokokin gyaran haraji guda hudu da Majalisar Dokoki ta Kasa ke tattaunawa sun zama doka.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ne ya bayyana hakan yayin da yake magana a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels Tɓ, wanda wakilin majiyar mu ya sa ido a ranar Lahadi da daddare.

Jaridar Manhaja ta ruwaito cewa dokokin da ake tattaunawa sun haɗa da:

Dokar Kafa Hukumar Haɗin Kai ta Haraji ta Nijeriya, 2024 – SB.583; Dokar Kafa Hukumar Haraji ta Nijeriya, 2024 – SB.584; Dokar Gudanar da Haraji ta Nijeriya, 2024 – SB.585 da kuma Dokar Haraji ta Nijeriya, 2024 – SB.586.

Zulum, wanda ya ce shi ko wasu gwamnonin Arewacin Nijeriya ba su adawa da Shugaba Bola Tinubu kan wadannan dokokin, ya bayyana cewa suna buƙatar tattaunawa da ƙarin bayani don kada yankunansu su cutu.

“Wannan tsarin dimokuraɗiyya ne, muna buƙatar ƙarin lokaci. Wasu sun shaida wa Shugaban Kasa cewa gwamnonin suna adawa da shi, amma ba mu ce haka ba. Mun san ikon Shugaban Kasa, ni mutum ne mai biyayya ga tsarin mulki, ina girmama shi. Idan Shugaban Kasa ya yi niyya, zai iya tabbatar da dokokin, amma hakan yana da sakamako ga al’ummar ƙasa,” inji Zulum.

“Wani abu da dokar haraji ta tanada shi ne cewa daga shekarar 2029, TETFund za a rushe shi domin kamfanoni za su daina tallafa masa bisa doka… NASENI za a rushe daga 2029… NITDA za a rushe. Wadannan sune damuwarmu,” in ji gwamnan Jihar Borno.

Har ila yau, Zulum ya kara bayyana cewa idan dokokin suka zama doka, jihohi 34 na Tarayyar Nijeriya za su yi asara, yayin da Lagos da Riɓers za su fi cin gajiyar dokokin.

“Su kawo mana alkaluma da bayanai, su tabbatar mana,” in ji Zulum, yana gargadin cewa za a samu matsaloli ga ‘yan Nijeriya idan Shugaba Tinubu ya dage wajen tabbatar da dokokin ba tare da la’akari da sakamakon su ba.

By ukarofi