Gidan talabijin mai zaman kansa na farko a Nijeriya ya rufe sakamakon tsadar wutar lantarki 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Mahukunta a kamfanin Desmims Broadcasting Nigeria Limited, wanda yake da gidan talabijin DITV Kaduna da gidan rediyon Alheri sun sanar da dakatar da ayyukansu har sai baba-ta-gani.

Tashar Talabijin ɗin ita ce tasha mai zaman kanta ta farko da ta fara aiki a ranar 2 ga watan Yuni, 1994.

A wata sanarwa da muƙaddashin babban manajan gidan talabijin din, Idris Mustapha ya fitar a ranar Juma’a, ta ce an ɗauki matakin ne saboda tsadar wutar lantarki.

Sai dai ya ce matakin bai shafi gidan rediyon Alheri da ke Zariya ba.

Mustapha ya yi nuni da cewa, taɓarɓarewar tattalin arzikin da ake fama da shi a ƙasar nan ya sa samar da kuɗaɗen shiga ya zama ƙalubale ga ‘yan kasuwa da dama.

Yayin da ya ke nuna rashin jin daɗi da takura da rufewar zai haifar da miliyoyin masu saurare da kallon tashar, Mustapha ya ce gidan rediyon zai koma bakin aiki da zarar yanayin kuɗin shiga ya inganta.

By ukarofi