Dole mu rungumi fasahar zamani wajen yaƙi da matsalolinmu – Shettima

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya jaddada buƙatar amfani da dabarun fasahar zamani wajen yaƙi da ta’addanci, da manyan laifukan da ake aikatawa ta yanar gizo da ma sauran ƙalubalen tsaron kan iyaka a Nijeriya da Afirka baki ɗaya.
Shettima ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin kwamitin gudanarwa na sashen sarrafa bayanan sirri na 17 ƙarƙashin Cibiyar Nazarin Tsaro ta ƙasa (NISS).

Masu ziyarar suka ce Kwas ɗin ya mayar da hankali kan ” Samar da hanyoyin Ƙarfafa tattalin arziki a Afirka tare da daƙile Ƙalubalen da nahiyar ke fuskanta a fannin fasaha.

Shettima ya bayyana yiwuwar amfani da ƙirƙirarriyar basirar (AI) wajen magance batutuwan da suka shafi noma, kiwon lafiya, hada-hadar kuɗi, da tsaro.

Mataimakin ya kuma ƙarfafa gwiwar matasan Afirka da su shiga a dama da su a fannin basirar AI don samar da ci gaban nahiyar.

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma ambaci kamfanonin Nijeriya masu nasara, irin su Moniepoint, Interswitch, Flutterwave da OPay, a matsayin misalan ƙarfafa gwiwar ‘yan kasar a fannin ƙirƙire-ƙirƙire inda ya ƙalubalanci shugabanni da ƙara azama wajen ƙarfafa gwiwar yan ƙasa da himmatuwa wajen tunkarar ƙalubalen da Nijeriya da nahiyar Afirka ke fuskanta.

By ukarofi