Daga SUNUSI MUHAMMAD a Gusau
Ƙungiyar ci gaban matasan Zurmi a Jihar Zamfara sun yi Allah wadai da abin da su ka kira nuna halin ko in kula da gwamnatin Jihar Zamfara ke yi a fannin abubuwan more rayuwa da ke da alaƙa kai tsaye ga inganta rayuwar al’ummar garin Zurmi.
Mataimakin shugaban ƙungiyar, Abba Modibbo ya bayyana haka a wata hira da Blueprint Manhaja a Gusau yau Litinin.
A cewarsa, garin Zurmi ya shafe sama da shekaru biyar babu wutar lantarki, ya ƙara da cewa duk da kiran da suka yi ga gwamnatin jihar tun wanccan gwamnatin da ta gabata da Kuma mai ci yanzu kan lamarin amma hakan ya ci tura.
Ya kuma ƙara da cewa kimanin watanni shida da suka gabata ne ‘yan bindiga suka far wa garin inda suka lalata musu eriya ta hanyar sadarwa ta MTN, lamarin da ya sanya alummar garin cikin wani mawuyacin hali wajen sadar da zumunci a tsakanin ‘yan uwansu da ke wajen jihar.
Modibbo ya yi nuni da cewa sama da shekaru biyar kenan garin na Zurmi ke cikin mawuyacin hali na rashin ruwan sha wanda ke buƙatar gwamnatin jihar ta ɗauki mataki domin samun ingantaccen ruwan sha a yankin.
“Duk matsalolin da na ambata a baya gaskiya ne kuma gwamnan jihar Dauda Lawal yana da cikakkiyar masaniya game da lamarin amma mun ga ya zama dole mu gabatar da buƙatun mu ga gwamnatin jihar don gaggauta biyan buƙatun namu.” Ya ƙara da cewa
Modibbo ya kuma yi kira ga gwamnatin Jihar Zamfara da ta gaggauta kammala makarantar su ta koyon aikin jinya da ungozoma domin ci gaban yankin a kowane fanni na tattalin arziki.
“Ina so in yi amfani da wannan kafar in roƙi gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal da ya cika alƙawuran yaƙin neman zaɓen da ya yi wa al’ummar Zurmi ta hanyar magance dukkan manyan ƙalubalen da muke fuskanta domin al’ummarmu su ci moriyar mulkin dimokuraɗiyya a yankin. Yace .
