Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Uwargidan gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Hurriyya Dauda Lawal ta ƙaddamar da kwanaki 16 na fafutukar yaƙi da cin zarafin mata da ƙananan yara a Jihar Zamfara a yau Litinin. Ta bayyana cewa kariyar haƙƙin kowane yaro da mata shi ne abunda ta bai wa fifikon a ofishinta.
An gudanar da taron ne a ɗakin taro da ke gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.
A cewarta, nan ba da jimawa ba dokar hana cin zarafin jama’a (VAPP) za ta fara aiki sosai a jihar domin tabbatar da kare cin zarafin mata da ƙananan yara.
“Dokar VAPP na da nufin kawar da tashe-tashen hankula a tsakanin alumma da kiyaye cin zarafin mata da ƙananan yara don magance cin zarafin mutane musamman mata da yara ƙanana.” Ta ce.
Ta ƙara da cewa ofishinta zai ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da kare haƙƙin marasa galihu musamman mata da yara da Kuma nakasassu ta kowane fanni.
Wannan biki na shekarar bana za a kwashe kwanaki goma sha shida anayi a Jihar Zamfara, wanda zai kammala a ranar 10 ga Disamba kan cin zarafin mata. Hakan zai bamu damar kare haƙƙin ‘yan matanmu da yara masu rauni daga duk wani nau’i na cin zarafi na jinsi ta kowane ɓangare na ayyukan bil’adama a faɗin jihar.
Ta kuma ƙara da cewa tuni shirye-shirye sun kammala daga ofishinta don ɗaukar nauyin fassara kundin dokar cin zarafin mutum “VAPP Laws Gazette” zuwa harshen Hausa domin jama’ar jihar su fahimci muhimman abubuwan da ke cikinsa.
Hajiya Hurriyya Dauda Lawal ta ci gaba da bayar da tabbacin cewa ofishinta zai yi aiki tare da dukkanin masu hannu da shuni da ƙungiyoyi da cibiyoyin addini da masarautun gargajiya domin tabbatar da kare haƙƙin mata da ƙananan yara da masu buƙata ta musamman a jihar.
