‘Ƴan sanda sun ceto fasinjoji 14 daga hannun ƴan bindiga a Katsina

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’an ƴan sanda a Katsina sun yi nasarar ceto fasinjoji 14 daga harin ƴan bindiga a ƙauyen Ɗan’arau dake Magama a ƙaramar hukumar Jibia ta Jihar Katsina.

Kakakin ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu ya bayyana hakan cikin wata takarda da ya fitar, inda ya ce lamarin ya auku ne a ranar Lahadi.

Ya ce ƴan bindigar sun farmaki wasu motoci biyu ne akan hanyar da nufin garkuwa da su inda suka yi ta harbe-harbe.

A yayin haka ne ƴan sandan yankin suka samu labarin lamarin inda cikin hanzari suka kai ɗauki tare da yin ba-takashi da ƴan bindigar wanda hakan ya sa suka yi galaba akansu.

A sakamakon haka ne wasu mutum biyu suka samu raunuka inda aka gaggauta kai su asibiti don ba su kulawa.

Ya ƙara da cewa, jami’an suna cigaba da ƙoƙarin gano mafakar suaran ƴan bindigar a yayin bincikensu don kamo su.

A nasa jawabin, Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Aliyu Abubakar Musa ya yaba wa ƙoƙarin jami’an tare da kira a gare su da su ƙara ƙaimi wajen ganin an daƙile ayyukan ta’addanci a yankin.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su cigaba da bai wa jami’an bayanai da su taimaka musu wajen gudanar ayyukansu.

By Babaji