DSS da sojoji sun hallaka mayaƙan ɗan bindiga, Dogo Giɗe a jihar Neja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A wani  samame da ya zo da mamaki, rundunonin musamman na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS), tare da haɗin gwiwar dakarun sojojin Nijeriya, sun hallaka aƙalla ’yan bindiga 45 a yankin garin Kuchi da ke ƙaramar hukumar Munya, Jihar Neja.

Aikin ya gudana ne cikin sirri, kuma ya kasance wata babbar nasara a ci gaba da fatattakar ’yan bindiga a Jihar Neja, musamman mabiya fitaccen jagoran ’yan bindiga, Dogo Gide.

Manhaja ta rawaito cewa majiyoyin tsaro sun bayyana cewa DSS ta bi sahun ’yan bindigar inda ta hana su kai hari ga wasu ƙauyuka da Dogo Giɗe da magoya bayansa suka tsara.

Bisa bayanan sirri da aka samo daga sabbin ƙoƙarin bincike na ɓoye da hukumar ke yi, an gano cewa ’yan ta’addan da suka fito daga dajin Bilbis a ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara da kuma wasu sassan Jihar Kaduna, Dogo Giɗe ne ya gayyace su domin kai hari a yankin Kuchi.

Majiyar tsaro ta ce: “Da safiyar Litinin, 2 ga Yuni, 2025, ’yan bindiga kusan 100 daga jihohin Kaduna da Zamfara, ɗauke da makamai masu linzami, sun nufi garin Kuchi da nufin kai hari ga al’umma da ke can.

“Amma jami’an tsaro sun kai wa ’yan bindigar hari cikin mamaki a wajen garin Kuchi kafin su samu damar fara harin da suka shirya.

“An yi musayar wuta da ’yan bindigar da suka fara tserewa, wanda hakan ya haifar da kashe da dama daga cikinsu, wasu kuma sun jikkata sosai. Haka kuma an ƙwato babura da dama da kuma harsasai.

“Duk da haka, jami’ai biyar na DSS sun ji munanan raunuka kuma suna jinya a asibiti a halin yanzu, kamar yadda majiyar ta tabbatar.”

By ukarofi