DSS ta gurfanar da Malami da ɗansa a kotu kan zargin ɗaukar nauyin ta’addanci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Talata ne Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) ta gurfanar da tsohon Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Ƙasa, Abubakar Malami (SAN) tare da ɗansa a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin su da ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci.

An gurfanar da waɗanda ake tuhumar ne a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, inda suka musanta hannu a laifuka biyar masu alaƙa da ta’addanci da DSS ɗin ta gabatar akansu.

A cewar takardar ƙorafin, ana zargin Malami da ɗaukar nauyin ta’addanci a lokacin da yake riƙe da muƙamin babban lauya na ƙasa ta hanyar ƙin gurfanar da masu ɗaukar nauyin ta’addanci da aka gabatar da takardun ƙorafe-ƙorafensu a ofishinsa domin ɗaukar matakin shari’a a kansu.

DSS ta kuma zargi Malami da ɗansa da hannu a kitsa ƙaddamar da ayyukan ta’addanci da mallakar makamin Sturm Magnum 17-0101 ba tare da samun lasisi daga hukuma ba.

Har yanzu dai ba a samu wani bayani ko martanin Malami ko lauyoyinsa ba dangane da al’amarin ba.

Ana sa ran kotu za ta ci gaba da sauraron shari’ar domin tantance gaskiyar lamarin tsohon ministan, wanda da fari EFCC ta gurfanar da shi akan zargin badaƙalar kuɗaɗe.

By Babaji