NECO: Kaso 80 sun yi nasara a sakamakon jarrabawar 2025

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Jarrabawa ta Kasa (NECO) ta sanar da fitar da sakamakon jarrabawar SSCE na ɗalibai na musamman, wato ‘External’ na 2025, inda ta bayyana cewa sama da kashi 80 na ɗaliban da suka rubuta ta sun samu aƙalla kiredit biyar zuwa sama.

Rijistara kuma Shugaban hukumar, Farfesa Ɗantani Wushishi a wata hira da manema labarai a hedikwatar NECO da ke Minna a Jihar Neja, ya ce an kammala tantance sakamakon cikin nasara kuma tuni aka ɗora su a shafin hukumar domin dubawa.

Ya bayyana cewa, jimillar ɗalibai 96,979 ne suka yi rajista, yayin da 95,160 suka zauna jarabawar a fadin ƙasar.

A darasin Turanci, daga cikin 93,425 da suka rubuta, 73,167 sun samu credit ko sama da haka, wanda ya kai kashi 78.32. A Lissafi kuma, daga cikin 93,330, 85,256 sun samu credit, wanda ya kai kashi 91.35.

NECO ta kuma ce, ɗalibai guda 68,166 sun samu biyar na credits ciki har da Turanci da Lissafi, yayin da 82,082 suka samu kiredit biyar na waɗanda ba a haɗa Turanci da Lissafi ba.

Farfesan ya ƙara da cewa, an kama ɗalibai 9,016
da laifin satar jarrabawa, lamarin da ya nuna an samu ƙaruwa akan na 2024.

Akan haka ne ya ce hukumar za ta ɗauki matakin ladabtarwa akan cibiyoyi da masu sa ido da aka samu wani da hannu acikin aikata irin laifi.

Kazalika ta shawarar ɗalibai da za su ziyarci shafin www.neco.gov.ng domin duba sakamakonsu kai tsaye.

By Babaji