Daga JOHN WADA, a Keffi
Ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Nasarawa a inuwar jam’iyyar APC mai ci a jihar, Farfesa Muhammed Sani Haruna ya ƙaddamar da wani aikin fara gina wani hanyar karkara da ya haɗa ƙauyukan Keffin-shanu da Gwagwa abbreviations da Takalafiya da Unguwar Gwandara duk a ƙananan hukumomin Karu da Nasarawa a jihar ta Nasarawa da nufin inganta harkokin kasuwanci da zirga-zirga a yankin.
Da yake jawabin sa a wajen taron wanda aka gudanar a ƙauyen Keffin-shanu, ɗan takarar gwamnan Farfesa Muhammad Sani Haruna ya bayyana cewa wannan aiki na daga cikin ayukan agaji da yake gudanar wa bil’adam baki ɗaya ba tare da bambancin addini ko siyasa ko kuma ƙabila ba inda ya buƙaci waɗanda za su amfana da aikin su tabbatar sunyi amfani da hangar yadda yakamata.
A nasa ɓangaren shugaban taron Dr. Abdullahi Adamu ya bayyana Farfesa Muhammed Sani Haruna wanda shine kuma Sarkin Sharifan jihar ta Nasarawa a matsayin shugaba mai hangen -nesa da kuma tausayin al’umma musamman idan akayi la’akari da ire-iren waɗannan ayyukan cigaba da yake kawo wa yankunan karkara.
Dr. Abdullahi Adamu ya kuma buƙaci wanda aka bai wa kwangilar gina sabon hanyar ya tabbatar ya kammala aikin cikin lokaci ba tare da jinkiri ba inda yayi gargaɗin cewa tabbas za a hukunta ɗan kwangilar idan ya kasa cimma kammala aikin akan lokaci da aka keɓe masa na aikin.
Dr. Adamu ya ƙara da cewa tabbas idan aka kammala aikin za a samu bunƙasan harkokin kasuwanci da walwalar jama’a a yankin inda ya buƙaci ‘yan karkaran da ake musu aikin su yi duka mai yiwa wajen kulawa da aikin daga farko har ƙarshe.
A ƙarshe sai shugaban taron wato Dr. Abdullahi Adamu ya kuma yi amfani da damar inda yayi kira na musammam ga duka masu hannu da shuni a jihar musamman ‘yan takarar kujerar gwamnan jihar ta Nasarawa su yi koyi da Farfesa Sani Haruna a fannin aiwatar da ire-iren wannan manyan aiki wa al’umma dake karkara don suma susan ana yi da su.
Suma da suke tofa albarkacin bakin su, wasu manyan mutane da suka halarci taron da suka da Hon. Tanimu Adapson, da wasu mambobin majalisar dokokin jihar su biyu dake wakiltar yankin da shugaban ƙaramar hukumar Karu da sauran su duk sun yaba wa sarkin Sharifan dangane da aikin gina hanyar don amfanar al’ummar karkara baki ɗaya.
Abubuwa da aka gudanar a ƙarshen taron sun haɗa da hawan katapila da Farfesa yayi don nuna farawar aikin a hukumance da ɗaukan hotuna da sauran su.
