
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata Babbar Kotu a Jihar Kano, ta sanya ranar 15 ga watan Afrilu, 2026 a matsayin lokacin da za ta yi hukunci akan shari’ar da ake tuhumar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da wasu da hannu a sauya akalar wasu kuɗaɗe.
Ana tuhumar Ganduje da matarsa tare da wasu mutane da kamfanoni da hannu a laifuka 11 da suka haɗa da karɓar rashawa, haɗin baki, almundahana da karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai biliyoyin naira.
Sauran sune: Abubakar Bawuro, Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd, da kuma Lasage General Enterprises Ltd.
A zaman kotun, lauyoyi daga ɓangarorin shari’ar sun sanar da kotu game da buƙatun shari’a daban-daban da suka shigar ciki har da neman dakatar da cigaba da shari’ar da kuma ƙin amincewa da tuhumar ɓangarorin.
Alƙali da ke hukunci akan shari’ar, Amina Adamu Aliyu, ta ɗage zaman har zuwa ranar da za a saurari dukkan ƙorafe-ƙorafe da buƙatun da ke gaban kotu.
