‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Lamarin ya faru a garin Doma da ke ƙaramar hukumar Faskari inda yanzu haka anyi wa waɗanda suka rasu sutura ,su kuma waɗanda su ka samu raunuka daban daban a kwashe su zuwa asibiti.
Haka kuma wasu mazauna garin sun gudu ba a san inda suka yi ba.
Bayanai sun nuna cewa yan bindigan sun shiga garin ne da rana tsaka a lokacin da wasu mutanen garin sun taru wajen rabon gado na gidan marigayi Ashiru Gari Doma.
Nan take yan bindigan sukai ta harbe harbe tare da banka wa gidaje wuta.
Bayanai sun nuna cewa ‘yan bindigan sun kona kusan rabin garin da kasuwanni.
Sun kuma kashe limamin garin da mai garin Doma da kuma wani babban ɗan kasuwa wanda kuma shugaban kwamitin tsaro ne na garin.
Har ya zuwa yanzu babu wani bayani daga jami’an tsaro ko gwamnatin jihar Katsina.
Halin da ake ciki yanzu mutanen garin na zaune cikin fargaba tare da kira da gwamnatin Katsina da na tarayya da su gaggauta kai masu ɗauki da jami’an tsaro.
