Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar tsaro ta DSS ta kama sama da buhu 2,000 na shinkafar tallafin Gwamnatin Tarayya ta bayar a raba wa talakawa a hannun wasu da ake zargin sun karkatar ne a Jihar Katsina.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Gwamnatin Tarayya ta ba da tirela 20 na shinkafa domin raba wa talakawa, da nufin rage musu raɗaɗin yunwa da tsadar rayuwa.
Jami’an DSS sun kama waɗanda ake zargin sun karkatar da shinkafar da ya kamata a raba wa talakawan jihar ne a Babbar Kasuwar Katsina.
A daren ranar Laraba ne DSS ta kama ’yan kasuwan da ake zargi, inda jami’an hukumar suka iske shagunan mutanen cike da shinkafar tallafin.
Wasu dai na zargin ba za a rasa hannun wasu jami’an gwamnati a wannan badaƙalar ba.
